Abinda ya faru bayan Da yace min shi Dillalin motoci ne bayan aurammu na gane baka Nike ne

0

Tofa! Abinda ya faru bayan Da yace min shi Dillalin motoci ne bayan aurammu na gane baka Nike ne Innalilahi

Jaridar Dimokuradiyya ta rawai to cewa Wata Matashiya a Najeriya ta bayyana irin halin da wata kawarta ya shiga bayan wani damfarar kalamai da wani saurayi ya yi mata lokacin suna nema.

Matashiyar mai suna Fairy Gbemie ta bayyana cewa mijin kawar tata ya sharara mata karyar cewa shi dillalin motoci ne, to amma bayan sun yi aure ta gane cewa ashe Makanike ne.

Related Posts
1 of 405

Ko da yake bata bayyana sunan kawar tata ba, amma bisa la’akari da Kalamanta ta nuna cewa yana zirga-zirga cikin motoci daban-daban lokacin da yake zuwa wurin ta.

Duk da cewa har kawo yanzu ba ta bayyana tsawon lokacin da suka shafe a tare ba, amma galibin jama’a na hasashen cewa wannan aure ba lallai ne ya yi karko ba.

Da ma dai a irin wannan zamani yan mata da dama na kasancewa ne a sahun ma’abota samun wurin hutu a rayuwarsu ta aure, to amma an ce tabbas idan da kwadayi lallai akwai wulakanci.

Kada kumanta kudanna mana Alamar kararrawar sanarwa domin samun jin kararrawar sanarwar shirye-shiryenmu Masu ƙayatar wa mungode.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More

Privacy & Cookies Policy