Adam A, Zango Yayi Bayanin Dalilin Da Yasa Ya Rungume Mace A Cikin Shirin Fim Din Asin Da Asin.

0

Adam A, Zango Yayi Bayanin Dalilin Da Yasa Ya Rungume Mace A Cikin Shirin Fim Din Asin Da Asin.

Adam A, Zango Yayi Bayanin Dalilin Da Yasa Ya Rungume Mace A Cikin Shirin Fim Din Asin Da Asin.

‘YAN HAUSA FILM SUNA NEMAN WUCE IYAKA

Wannan sakon ya shafi bangaren su jarumin Hausa film Adam A. Zango da bangaren su S. Bono

An ja hankalina bisa wasu munanan wakoki na fitsara da rashin albarka da suka fitar tare da wasu ‘yan mata sanye da wanduna damammu babu dan kwali a kansu, sun sanya gashin doki sai kace ba ‘ya’yan Musulmai ba

S. Bono kace kai Malami ne ko Dalibin Ilimi, ka taba koyarwa a Islamiyya, amma saboda neman duniya ta hanyar da bata dace ba ke jefar da Maluntar naka, ka nemo ‘yar mutane ka sata rawa da waka babu dan kwali a kanta kuma tana sanye da wando

Zan bada Misali da fim din Izzar So, tauraruwar film din mai sun Nana tana burge mutanen kirki, saboda kullun tana cikin hijabi tana jan ayoyin Qur’ani da Hadisai, kun sa ta tana koyar da dabi’u na kwarai a film din

Amma gashi nan daga karshe kun rusa mata martaba da kamala, kun sakata cikin waka na iskanci babu dan kwali a kanta tana sanye da wando damamme.

Abinda ku keyi wuce makadi da rawa ne, fitsara ne zalla da rashin kunya, na tabbata ba zaku iya aikata haka da ‘ya’yan cikin ku ba, yanzu kai tsaye kun koma kwaikwayon abinda turawa da yahudaa sukeyi, kuma kunce kuna koya mana tarbiyya ne.

Related Posts
1 of 407


Muna kira ga hukumomi masu sanya ido akan ‘yan film da mawaka, ya kamata a takawa abinda su Adam A. Zango, S. Bono Hamisu Breaker sukeyi a cikin wakokin fitsara.

Muna fatan Allah Ya shiryar da su

WAI SUN WAYE.

Ni kuma banga abin burgewa da wayewa anan ba, sai dai na ga zallan rashin kunya, rashin tarbiyya da rashin mafadi.

Dabi’un yahudu da nasara irin wannan ko Musulmi ya koya baya masa kyau, karshensa nadama ne.

Da hankalina da wayona da addinina na Musulunci ba zan iya aikata haka da kowace irin mace ba balle matar da zan aura, balle kuma na dauka a hoto na yada a duniya.

Kwanaki na ji wani Malami yana cewa saurayi da budurwaa da suka tashi zasuyi aure suna kwashe albarkan auren tun a gurin daukar hoto kafin aure saboda abubuwa na wuce iyaka, haram da sabon Allah da suke aikatawa

Ko ka biya sadaki tunda dai ba’ayi siga ba, kuma babu shaidu to baka da lasisin da zaka rungumeta, ko ka tsotsi bakinta a dalilin daukar hoto kafin aure, aikata hakan laifine babba, kuma yana kwashe albarkan aure

Allah Ka shiryar da su

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More

Privacy & Cookies Policy