An ɗaura: Jarumin Kannywood Yusuf Saseen ya zama angon Amina –
Yusuf Saseen da Amina cike da farin ciki jim kaɗan bayan an ɗaura auren su
ƘARSHEN tika-tika, tik! Jarumin Kannywood Yusuf Muhammad Abdullahi (Saseen) ya zama ango.
A yau Asabar, 24 ga Disamba, 2022 aka ɗaura auren sa da masoyiyar sa Amina Zakari Yunusa Daya.
An ɗaura auren da misalin ƙarfe 11:00 na safe a gidan Makaman Fika da ke layin makaranta a garin Potiskum cikin Jihar Yobe, a kan sadaki N50,000.
Bayan ɗaurin auren an yi walima.
Ango tare wasu daga cikin mahalarta ɗaurin auren
Wasu daga cikin ‘yan fim da su ka halarci ɗaurin auren su ne Ahmad Bello (Naziru a ‘Daɗin Kowa’), Aminu Saira, Umar UK, Ibrahim Birniwa, Isah Ferozkhan, Aminu Unguwar Gini, Yasin Auwal, Sani Mai Iyali, Murtala Sani da Ahmad Nagudu.
Gobe kuma in Allah ya kai mu lafiya za a yi dina a Kano.
Allah ya ba su zaman lafiya da zuri’a ɗayyiba, amin.
Yasin Auwal, Umar UK da Aminu Saira a wurin walima
Yusuf Saseen yayin da zai shiga mota zuwa wurin ɗaurin aure