An Kama Matasan dasuka ƙwaƙulewa wani almajiri ido

0

Rundunar ƴan sandan jihar Bauchi na neman matasan dasuka ƙwaƙulewa wani almajiri ido ruwa a jallo

Yan sanda a jihar Bauchi sun ce suna gudanar da bincike game da wani hari mai tayar da hankali a kan wani yaro ɗan shekara 12 da aka samu, an ƙwaƙule masa ido ɗaya. Wata sanarwar ‘yan sanda ta ce wasu mutane baƙin fuska su biyu ne a kan babur suka yaudari yaron wanda almajiri ne suka kai shi bayan garin Kafin Madaki, inda ƙarfi da yaji suka ƙwaƙule masa idonsa na dama. ‘Yan sandan jihar Bauchi sun ce maharan da suka ƙwaƙule wa yaron ido sun yi tafiyar su, inda suka bar shi cikin jini a bayan gari.

Sanarwar mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi SP Ahmed Mohammed Wakili ta ce yaron ɗan asalin jihar Kano yana karatun allo ne a Kafin Madaki lokacin da mummunan harin ya faru a kansa ranar Juma’ar da ta wuce.

Ta ce wurin da aka yi wa yaron aika-aikar ba shi da nisa da makarantarsu.

Tun farko a cewar wannan sanarwa, mutanen waɗanda ba a san su ba sun je ne a kan babur inda suka ɗauke shi da zimmar zai kira musu wata mata a cikin wani gida da ke kusa.

Related Posts
1 of 408


Ta ce a cikin wannan halin ciwo ne yaron ya yi ƙoƙari har ya kai inda abokan karatunsa suka gan shi, inda suka ɗauke shi suka garzaya da shi wurin malaminsu.

Bayan an kai ƙorafi ofishin ‘yan sanda ne kuma aka nufi asibiti da shi.

Sanarwar ta ba da tabbacin cewa ‘yan sanda na nan suna ƙoƙarin kama waɗanda suka aikata wannan abu.

Babu masaniya kan abin da ya sa maharan suka ƙwaƙule idon yaron sai dai a ‘yan shekarun nan ana samun rahotannin yadda ake cire sassan jikin mutane don yin tsafi. A farkon wannan shekara ma, an cire wa wani yaro idanuwansa biyu a jihar ta Bauchi.

Kada kumanta kudanna mana Alamar kararrawar sanarwa domin samun jin kararrawar sanarwar shirye-shiryenmu Masu ƙayatar wa mungode.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More

Privacy & Cookies Policy