Arna Sun Fi Musulmi Tausayi, Inji Zee-Zee
Rahoton Mujallar Fim
FITACCIYAR jaruma Ummi Ibrahim (Zee-Zee) ta bayyana cewa ‘yan Nijeriya waɗanda ba Musulmi ba sun fi takwarorin su waɗanda ba Musulmi ba jinƙai.
Ta ce ta gane haka ne daga abin da ya faru a gare ta a makon jiya lokacin da ta yi barazanar za ta kashe kan ta saboda damfarar da aka yi mata ta kuɗi naira miliyan 450.
Zee-Zee ta ce lokacin da abin ya faru, yawancin Hausawa ko ‘yan Arewa Musulmi daga masu ƙaryata ta sai masu zagin ta, amma su kuwa ‘yan Kudu waɗanda ba Musulmi ba, waɗanda ta kira “arna”, su ne masu tausaya mata da jajanta mata.
Daga nan ta yi tir da waɗanda su ka zage ta ko su ka ƙaryata ta a kan wannan lamari.
A makon jiya ne dai jarumar ta Kannywood ta bayyana cewa wani Inyamiri ya zambace ta zunzurutun kuɗi har naira miliyan 450, kuma faruwar hakan ya sanya ta yanke hukuncin gara ma ta kashe kan ta ta huta.
Labarin da ta bayar da muguwar shawarar da ta yanke wa kan ta sun jawo ce-ce-ku-ce sosai a soshiyal midiya.
A sabon saƙon da ta tura ɗazu domin yi wa masu tausaya mata godiya, Zee-Zee ta ce: “Salam ‘to Nigerians’, ina son ku ban dama in gode muku a bisa jaje da ku ka min ta hanyar kira na a waya da aiko min da ‘text’ dangane da damfara na da aka yi na kuɗi masu yawa naira ‘million’ ɗari huɗu da hamsin a kan wani ‘business’ da za mu yi na saye da sayarwa na ƊANYEN MAI da wani Inyamuri da ke Lagos.
“Ya damfare ni a kan ‘business’ da za mu yi da shi, amma maƙiya na saboda jahilci da hassada sai su ke cewa ba wani damfara na da aka yi, ƙarya ne. To Aljanna za a sa ni a ciki ko ko zunubai na za a yafe min da zan yi ƙarya in ce an damfare ni bayan kuma ba a damfare ni ba?
“To ya kamata mu Hausawa mu koyi son junan mu domin duk Musulmi ɗan’uwan Musulmi ne.
“Da aka damfare ni, akwai wani ‘page’ mai suna @instablog9ja, su ma sun yi ‘posting’ damfara na da aka yi, amma wallahi da na shiga ‘page’ ɗin ban ga ana zagi na ba, sai addu’a kawai da ake min da kuma ban haƙuri a kan damfara na da aka yi. Wasu ma ‘direct’ su ka dinga kira na su na jajanta min.
“Kuma fa shi mai ‘page’ ɗin instablog9ja ɗin wallahi da shi da ‘followers’ ɗin nasa duk yawanci arna ne ‘yan Kudu.
“Amma a nan Arewa kuma duk wani ‘page’ da aka yi ‘posting’ damfara na da aka yi to zagi na kawai ake yi. Abin ya ban haushi.
“Ba zagi na da aka yi ba ne ya ban haushi; abin da ya ban haushi shi ne a ce ina Musulma ƙaddara ya same ni amma sai arna ne wanda addinin mu ba ɗaya ba su ne za su nuna alhinin su a kan damfara na da aka yi?
“Sai yanzu na fahimci arnan Nijeriya wallahi sun fi Musulman Nijeriya tausayi. Don haka Allah wadaran Musulmai masu irin wannan mummunar zuciyar!”
Zee-Zee ta miƙa godiyar ta ga ƙanwar ta, Hasina Ɗan-chaina, “da ta zo Kano ta taka min birki ta hana ni aikata SUICIDE da na ce zan yi.”
Tsohuwar jarumar ta faɗi dalilai uku da su ka sa ta ƙudiri aniyar kashe kan ta ɗin. Ta ce: “Tabbas, na so na kashe kai na ɗin domin abu 3 su na damu na. Na 1, mutuwan baba na; na 2, ina son wani namiji da ya mutu; na 3, damfaran da aka min.”
Bugu da ƙari, ta gode wa wasu da ta kira “manyan mutane iyayen gida na da su ka dinga aiko min kuɗi ta ‘account number’ na domin in rage asaran damfaran da aka min.”
Daga nan ta yi tuba ga Allah kan muguwar niyyar da ta ɗaura.
Ta ce, “Sai magana ta ƙarshe kuma, ina tuba ga Allah dangane da kai na da na ce zan kashe. Astagfirillah ya Allah!”
Idan kun tuna, mujallar Fim ta ruwaito cewa a cikin ‘yan watannin nan Zee-Zee ta riƙa wallafa hotunan shahararren mawaƙin nan Michael Jackson a kai a kai, tare da kalamai masu bayyana shauƙin so game da shi.
Akwai yiwuwar kila shi ne namijin da ya mutu wanda ta kamu da ciwon son shi, kuma da ta haɗa da rasuwar baban ta da damfarar da ta ce an mata sai abin ya haifar da tunanin ɗaukar ran ta shi ne mafita daga ƙuncin da ruhin ta ke ciki.