Aure: Adamsy Celebrity da Ummakatty sun zama tif-da-taya

0

Aure: Adamsy Celebrity da Ummakatty sun zama tif-da-taya - Kannywood - News, reviews and more › hausa

Amarya Ummu-Khursum Muhammad Tamula (Ummakatty) da Adam . Adam (Adamsy Celebrity) a wajen dinar auren su

JARUMI a Kannywood, Adam A. Adam, wanda aka fi sani da Adamsy Celebrity, ya yi bankwana da kwanan shago.

A ranar Asabar, 10 ga Disamba, 2022 aka ɗaura auren sa da sahibar sa, Ummu-Khursum Muhammad Tamula (Ummakatty).

An ɗaura auren ne da misalin ƙarfe 11:00 na safe a masallacin Zawiyya da ke Zololo, Jos, Jihar Filato, a kan sadaki N350,000.

Related Posts
1 of 408


Ango da amarya a wurin ‘cocktail party’

Kafin ranar ɗaurin auren, an gudanar da shagulgulan biki irin su ‘cocktail party’, ƙwallon ƙafa, dina da Ranar ‘Yan Wasa.

‘Yan fim da mawaƙa da su ka halarci bikin sun haɗa da Ado Gwanja, Hamisu Breaker, Kawu Ɗansarki, Ɗanmusa, Al-Amin Buhari, Abubakar S. Shehu, Ahmad Delta, KB International, Tynking Mai Gashi, Yamu Baba, Gombe, Ahmad Shanawa, Aminu S. Bono, Umar Big Show, Yunusa Mu’azu, Abba Sadau, Bello Muhammad Bello, Z Square, Geena, Bilkisu Abdullahi, Maryam Yola, Ummi Ƙarama, Zainab Ishola, A’isha Channel 7, Murja Ibrahim Kunya da Zainab Sambisa.

Allah ya ba su zaman lafiya da zuri’a ɗayyiba, amin.

Amarya Ummakatty da ango Adamsy Celebrity
Ango Adamsy da abokin sa Tynking Mai Gashi a wurin ‘cocktail party’
Ango Adam da Ummu-Khursum a wurin dina.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More

Privacy & Cookies Policy