Ba da yawuna Lauyana ya nemi a yi min sassauci ba – cewar Sheikh Abduljabbar Kabara

0

Tofa! Ba da yawuna Lauyana ya nemi a yi min sassauci ba - cewar Sheikh Abduljabbar Kabara

Kotu ta ce, ta samu Abduljabbar Kabara da laifin yiwa ma’aiki (s a.w) kage da cin mutumcin ma aiki da cewar yayi fyade,

An same shi da laifi karkashin sashe na 382 (B)

Related Posts
1 of 407


Lauyan da ke kare shi Barrister Aminu Abubakar yace ayi masa sassauci saboda kuskuren fahimta ce tasa Malam Abduljabbar ya aikata wannan laifi.

Amma nan take malamin ya miƙe ya ce shi dai ba da yawunsa ba, Lauyana yake magana.

Malamin ya ce, baya neman sassauci, kuma yana neman a gaggauta yi masa hukunci domin zai yi mutuwa ta girma.

Ku ci gaba da bibiya, zamu ci gaba da kawo muku yadda take kasancewa.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More

Privacy & Cookies Policy