Babban buri na game da ‘ya ta, Surayya – jaruma Hadizan Saima

0

Babban buri na game da ‘ya ta, Surayya – jaruma Hadizan Saima - Kannywood - News, reviews and more › hausa

Surayya Salisu Yahaya

JARUMAR Kannywood Hadiza Muhammad, wadda aka fi sani da Hadizan Saima, ta yi addu’ar Allah ya kawo wa ‘yar ta Surayya Salisu Yahaya miji nagari.

Hadiza dai ta yi wannan addu’ar ne a hirar ta da mujallar Fim kan bikin shagalin bikin zagayowar ranar haihuwar ‘yar tata da aka yi a Kano.

A shekaranjiya Lahadi, 1 ga Janairu, 2023, jarumar ta shirya wa ‘yar ta Surayya bikin.

Surayya ta yi wasu zafafan hotuna masu ɗaukar hankali.

Related Posts
1 of 405

‘Yan fim da dama dai sun ɗora hotunan a shafukan su don taya ta murna tare da yi mata fatan alheri.

Da ta ke yi wa mujallar Fim ƙarin bayani a game da wannan abin farin ciki na ‘yar ta, Hadiza Muhammad ta ce: “Lallai babu abin da zan ce da Allah sai godiya da ya nuna mani wannan rana domin wannan abin farin ciki ne a gare ni.

Surayya

“A yanzu babban burin da na ke fata shi ne Allah ya nuna mani lokacin auren ta. Ina fatan Allah ya ba ta miji nagari, kuma Allah ya ƙara mana shekaru masu albarka cikin ƙooshin lafiya da kwanciyar hankali.”

Mujallar Fim ta ruwaito cewa jaruman Kannywood a yanzu duk girma ya kama su daga don haka a yanzu sun koma bikin ‘ya’ya da jikoki. A yanzu ko bikin zagayowar ranar haihuwa wasu jaruman sun daina yin nasu sai dai na ‘ya’yan, kamar yadda ya faru ga Hadizan Saima.

Surayya a hotunan zagayowar ranar haihuwar ta
Lokaci ya yi: Burin Mama Hadiza shi ne ta ga auren ‘yar ta
Hadizan Saima

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More

Privacy & Cookies Policy