Bayyanar Wannan Halitta A Cikin Jama’a Ya Tada Hankalin Al’umma, Idan Bakada Tsoro Kalli Videon 

0

Subhalallah: Bayyanar Wannan Halitta A Cikin Jama'a Ya Tada Hankalin Al'umma, Idan Bakada Tsoro Kalli Videon

Subhalallah: Bayyanar Wannan Halitta A Cikin Jama’a Ya Tada Hankalin Al’umma, Idan Bakada Tsoro Kalli Videon

~Blood Waterfall! Ɓulɓulowar Jini Daga Kan Dutse.

Antarctica daya daga cikin continent ne guda bakwai da muke dasu a duniya, amma tana da abin al’ajabi da mamaki, wanda har yau masana kimiyya basu gano su ba.

Kashi casa’in da tara (99%) na Antarctica kankara ne, da sanyi mai tsanani, kashi daya (1%) ne kaɗai busashshen wuri (dry land). Karkashin wannan kankaran mai girma, akwai sirruka dayawa da ba’a gano su ba, wasu daga cikin masana suna riya cewa akwai yiwuwar wani gari ne mai girma mai suna Atlanta aka birne karkashin kankaran, wanda suke kira da turanci “The Lost City Of Atlantic”.

Kuma wani abin mamaki shine, ɓulɓular ruwan jini daga duwatsun kankara, wanda suke zubowa kamar waterfall, Kuma duk da sanyin da akeyi a wurin, wannan ruwan jinin bai daskare ba! Lallai akwai darasi anan ga masu tunani. Da kuma wasu dabbobi wanda halittu ne daban da wanda muka saba gani. Wasu akan cikunansu suke tafiya, kamar yadda Allah Yace; “Kuma Allah ne Ya halitta kõwace dabba daga ruwa. To, daga cikinsu akwai waɗanda ke tafiya a kan cikinsu…” (An-Noor:45.

Hakika Allah Yayi kira garemu acikin Al-Qurani dacewa; “Shin, ba su yi tafiya ba, a cikin ƙasa, dõmin su gani yadda ãƙibar waɗanda ke a gabãninsu ta kasance? Allah Ya darkãke a kansu. Kuma akwai misãlan wannan ãƙibar ga kãfirai (na kõwane zãmani).” (Muhammad:10

Idan dai ta tabbata akwai wasu waɗanda aka halaka a karkashin dutsen kankaran nan, to tabbas waɗan nan sun ɗanɗana azaba mai raɗaɗi, kuma darasi ne garemu, wannan iko ne daga cikin ikon Allah.

أَفَلَمْ يَسِيرُوا فِي الْأَرْضِ فَتَكُونَ لَهُمْ قُلُوبٌ يَعْقِلُونَ بِهَا أَوْ آذَانٌ يَسْمَعُونَ بِهَا ۖ فَإِنَّهَا لَا تَعْمَى الْأَبْصَارُ وَلَٰكِن تَعْمَى الْقُلُوبُ الَّتِي فِي الصُّدُورِ

Ita labarin “Atlanta” ko ince “Lost City Of Atlantic” ta samo asali ne daga wani ɗan falsafa da ake kira Plato. Ya bada labarin ne a shekarar 360 B.C. Ya bada labarin ne da cewa, kasar Atlantar ta kasance ta kware wojen yaki akan ruwa, tana da arziki, da zinari, kuma suna rayuwa ne akan sibiri, daula ne mai tsananin karfi da girma, tana aikata fasadi da ɓarna a doron kasa, sai Ubangijinsu ya halaka su ta hanyar nutsarwa. Idan wannan labarin ta tabbata, to mu dai munsan Allah ne ya dammara su, saboda zunubansu, kuma yabar aya ga mu da muka zo bayansu.

«Ku duba karkashin ɗaya daga cikin hotunan nan nayi ɗan karin bayani, gameda jan ruwan dake ɓulɓulowa daga dutsen»

Allah Ya tsare mu, Ya sa mu kyautata tamu rayuwar, ta yadda duniyar mu, da lahirar mu, bazata zame mana nadama ko da nasani ba. Aameeen.

*📗MUMMUNAN ZATO 📗*

*NA*

*HALIMA ABDULLAHI K/MASHI*

Book 2

*page 1*

A hankali ta maida ƙofar ta rufe, sannan ta juyo da nufin ta ƙaraso cikin ɗakin. Idanu ta zare tare da dafa ƙirji, sannan ta ce “innalillahi” lokaci guda ta juya baya ta runtse idanu,duk ta yi haka ne sakamakon ganin Uncle ya fito daga wanka daga shi sai gajeren wando,yana goge jikinshi da tawul. Ta kama ƙofar zata buɗe, ya ce “Beby” ta ce “Umm.” Ta ce “bari….em….bari na dawo in ka gama ban san kana ciki ba ne,don Allah ka yi haƙuri.” Ya ce “Me ki kayi min? Ki zo kiyi aikinki,kin ji ko” ta juyo amma ƙasa take kallo tana tafiya ta ci karo da gado, da sauri ta ɗago idanunta ta sauke su akan gadon, cikin mamaki ta tsaya kallon gadon sam bai kai nata girma ba, kuma shinfiɗe yake da zanin gado an lailaye shi,ta ɗago kai ta kalli Uncle tayi sauri ta kuma sunkuyar da kai don ganin har yanzun bai saka riga ba, kuma bai damu ba sai shafa manshi yake yi. Cikin in ina ta ce “An….an ma riga an gyara ashe?” Ya dube ta,duk ta daburce. Ya ɗauki riga shirt fara mai gajeren hannu ya saka,ya tako zuwa hiring.

Related Posts
1 of 405

Ya kamo hannunta ya zaunar da ita yana riƙe da yatsunta cikin nashi kanta yana kallon ƙasa har yanzu bazata iya kallonshi ba saboda gajeren wandon bai rufe cinyoyinshi ba sannan duk cibiyoyinshi gashi ne, ya ɗan murza mata yatsun “Beby bai haramta ki ga tsiraici na ba,ko ni in ga naki ba” ta dube shi da sauri ya ce “Yes saboda ni da ke halalin juna muke” Ta sauke kanta ƙasa amma zuciyarta tana son ya fayyace mata komai don ita bata gane nufin shi ba,ya ce “yanzu dai Beby ni wanene a gurinki? Ma’ana menene matsayi na?” Ta dube shi sannan ta kuma sunkuyar da kai,a hankali ta ce “Miji” ya ce “me ake nufi da Miji? Ta yi shiru zuwa can ta ce “Wanda ya yi aure shi ne Miji” Uncle ya yi ɗan murmushi don jin shirmenta, ya ce to menene aure?” Ta ce “Aure?” Ya ce “Umh” ta ce kamar dai yanda ake yi mutane su taru a ɗaura shi kenan sai kuma a kai matar” ya ce “to daga nan fa?” Ta ɗan dube shi sannan ta rufe fuska, ya ce “Gaya min idan an kaita sai tayi me a gidan? Ta ce “zata rinka yin shara da wanke-wanke tanayin girki,ta rinƙa kula da yara.

Ya shafa hannunshi yana cewa, “Good, ashe kin sani? Ta yaya akeyi ta samu yaran?” Ta ce “Iye!’ Ya ce “Ya ya za’ayi ta samu yaran?” Ta ce, “Ita ce zata haife su.” Ya ce, “Haka nan zata haife su?” Ta ce “Eh,in cikinta ya yi girma.” Ya gyara zama don jin sun gangaro inda yake son ji, ya ce “To ya ya akeyi ciki ya fito mata?” Ta ɗan yi jim,can ta ce, “Nima ban sani ba,ƙila wani abinci ake ci.” Dariya ta kufce mishi, duk cikin matan da ya aura babu wadda ba ta san kan zaman aure ba kamar A’isha, duk da cewa akwai sa’arta cikin su, ya dube ta.

“Kina son ki san yadda ake a yi g?”

Kanta yana ƙasa ta ce, “Eh” ya yi ɗan murmushi ya ce, “In na tambaye ki abu ɗaya yanzun ba ki san shi ba, idan baki san shi ba,zan haɗa su in miki bayani. Amma in kin san shi to zan bar ki har ki sani da kanki,wato zai zama assignment,amma fa ba zaki tambayi kowa ba,kin yarda?” Ta ce”To ya ya za’ayi na sani in ban tambayi kowa ba?” Ya ce “Zaki sani,yau da gobe.” Ta ce “To yi tambayar in ji”. Ya ce “Kin san Haila? Da sauri ta saka kanta cikin cinyoyinta,don ya taɓo mata abinda ta fi jin kunya a rayuwarta,don in tana Haila ko Ummanta tana jin kunyar ta sanar da ita, sai dai ta yi ta nuƙu-nuƙu har Umman ta gano da kanta, ballantana Uncle wanda bata daɗe da saninshi ba,ba su yi sabon da zata yi mishi wannan maganar ba. Cikin dariya ya ce, gaya min mana Beby,kin taɓa yi ne? Miƙewa ta yi har tana cin karo ta fita da gudu

Ɗaki ta koma ta faɗa kan gado zuciyarta tana ta bugawa, ita dai tana matuƙar jin kunyar Uncle,shi bai sani ba ne zai mata wannan tambayar?.

Shiko dariya ya dinga yi,lallai dole ya haƙura da A’isha yanzu don ba ya son takura mata. Ya fi son a yi komai cikin sauƙi kuma cikin ilimi.

Jummai kuwa tana ɗaki cikin murna haka nan wani gefe sai ta ji ranta ya ɓaci, da tana da iko ko macen ƙuda ba zata yarda ta saukar mata a kan miji ba, balle mutum, shi yasa ta sha alwashin ko zata tafi tsirara ne sai ta halaka duk macen da ta ce zata zauna zaman aure da mijinta. Ta sani goben nan yarinyar nan ta zama gawa,don haka ita ranta kar yake, insha Allahu. Ƙwana ta yi tana kai-kawo cikin ɗakinta,don ba zata iya runtsawa ba.

A’isha tana zaune tana tasbihi , sai kurum taga an turo mata ƙofa da ƙarfi. Cikin tsananin firgita ta miƙe tsaye, ganin Hajiya Jummai tuni ta soma karato addu’a cikin zuciyarta. Hajiya Jummai ta yi sororo ganin A’isha tsaye. Ta ce, A’a, ihun wa nike ji? Sai na ji kamar kakari a nan ɗakin.” A’isha ta ce, “Kai,anya nan ne?” Ta ɗan yi tsaki tare da cewa, “Gaskiya ba nan ba ne.” Hajiya Jummai ta shiga waige-waige, zuciyarta tana mai tabbatar mata ihun A’isha ta ji, amma abin al’ajabi A’ishar ce gabanta tana mai tabbatar mata cewa ba a ɗakin ba ne. A’isha ta ce “Allah ba nan bane Hajiya.” Sannan ta ɗan rusuna ta ce, “ina ƙwana Hajiya?” Tsaki mai ƙarfi taja sannan ta fita a fusace, tare da sakin ƙofar da ƙarfi. Aisha ta yi shiru,a ranta tana son sanin me hakan ya ke nufi? Daga baya sai kurum ta taɓe bakinta gami da ɗaga kafaɗarta alamar su dai suka sani,ta koma ta zauna tana nazarin hirarsu da Uncle ta jiya. Daga bisani ta miƙe ta nufi kitchen ba don Uncle ba ne ya yi mata wannan tambayar game da Haila da zata ce ɗan iska ne,Don dai ta san halin Uncle shi ba ya iskanci. Uche ta samu yana aikinshi, suka gaisa sannan itama ta shiga haɗawa Uncle abin karyawa. Uche yana ɗan taya ta,ɗakinta ta nufa da tiren, tana shiga ta same shi zaune bakin gado cikin shirin fita. Ta dubi agogo,taƙwas saura ƙwata, ta ce Uncle har ka fito?” Ta dire tiren a gabanshi ta shiga haɗa mishi tea. Ta miƙa mishi sannan ta soma zuba mishi dankali da kwai tana saka mishi bota jikin bread,ya ce har fa na manta ina karyawa a gida,bari na sakko ƙasa Beby” ta miƙe ta ɗauko dardumar sallah ta shimfiɗa mishi, ya zauna ya shiga karyawa, sannan ta zauna tana gaishe shi. Ya amsa cike da jin daɗi, sannan ya ce “Ya gajiyar gudu jiya daga tambaya Beby sai ki ka gudu ko?”

Cikin cinyarta ta saka kanta,ta ƙi ɗagowa me zai sa Uncle ya dinga irin wannan maganar? Ai wannan kamar na ƴan iska ne. Ita fa ko a school ba ta wannan hirar da ƙawayanta,nata ganin bai dace ba.

Ya ce “shin wai Beby menene abin jin kunya? Ta ce “Uncle don Allah ni dai ka daina wannan zancan.” Ya ce “na daina Beby, shikenan?” Ta ɗaga kai alamun “Eh” ya ce “To oya ci abincin ki.” Ta ce, Uncle nifa sai anjima zan karya, wannan duk naka ne” Ya ce,ya ya zanyi da wannan Beby? Ai babu tsari ga kowane musulmi ya zauna ya yi mugun ci, Manzon Allah (S.A.W) yana kasa cikinsa kashi uku ne, ɗaya abinci, ɗaya ruwa, da kuma ya shaƙi numfashi dashi,don haka kin ga tunda da shi muke koyi, sai mu ma mu ƙwatanta. Zaka ci ka ƙoshi amma ta yanda ba zaka kasa tashi ba.

Aisha ta ce, “Haka ne.” Sai kusan tara ya fito daga ɗakin,yana son yarinyar ta shiga ranshi,ba ya gajiya da zama da ita yana son shirmenta,wani sa’in ta yi magana tamkar babba, wani sa’in kuma ta yi masa aikin ƙuruciya,waton shirme.

Kai tsaye ɗakin Jummai ya nufa,don yi mata sallama kamar yanda ya saba,in ba ya ɗakin ki zai zo ya yi miki sallama da safe in zai fita. Tana zaune abin duniya duk ya taru ya yi mata yawa, yanzun haka jin ta take yi tamkar ta yi hauka,don tsabar baƙin ciki. Ina ma kuka zai ƙwace mata ko zata samu sassauci. Sallamar maigidan ce ta dawo da ita cikin hayyacinta, tsayawa ya yi yana kallonta. Itama ta ɗago idanunta jajir tana dubanshi, ya ajiye jakar hannunshi ya nufi gurinta ya tsugunna a gabanta cikin sassanyar muryarshi, ya ce “Jummai” ya kamo hannunta, “wai shin Jummai me yake damunki ne cikin watannin nan duk kin rame kin lalace,dube ki don Allah sai ka ce wata tsohuwa?” Kalmar da tafi tsana kenan a kira ta da ita, wato tsohuwa. Hawayen da take ta so su zubo ko zata samu sauƙi suka ƙi zubowa, sai gasu yanzun sun zubo masu zafi ma,ta ce dole ne ka ce min tsohuwa tunda yanzun ka samu yarinya ƙarama wadda zata iya haihuwa,ba irina ba juya. Ya miƙe tsaye cike da jin haushi, “kinga matsalarki ko? Kin gani ko? Me yasa ne ke har kullum ba ƙya fahimta? Nifa ina son sanin matsalarki ne ba wai ina kushe ki ba ne,in baki son in san damuwarki Jummai ai sai in barki tunda ke ba ƙaramar yarinya ba ce. Ace kullum bawa ba zai sakawa zuciyarshi salama ba,koda yaushe sai baƙin rai. In kina da matsala ne ba sai ki faɗa min ba? Ta ce “Ni dai don Allah je ka kawai,ka bar ni inji da kaina.” Ya ɗauki jakarshi tare da cewa, “Allah ya ƙyauta.” Ya fita.

Ihu ta saka ita kaɗai,a ruɗe su Suwaiba suka shigo suna cewa, “Lafiya Anty Jummai?” Tana huci ta ce “ku bar ni zanci uban yarinyar can” Sofy ta ce, “Me tayi miki ne Anty? Yanzu mu je muci ubanta? Ta ce a’a ku bari ba yanzun ba,ni zan yi maganinta. (Waya ga sa kai a uku) Yinin ranar Jummai sun ƙule ita da Aminiyarta, suna neman mafita. Ta rantse ta kuma rantsewa cewa maigidan yana kusantar yarinyar gashi an ce zata mutu shiru bata mutu ba,ta dubi Kari,ko dai zan sa mata guba ne? Kari ta ce “a’a komawa zamu yi gurinsu.” Ta ce dibi asarar da na yi ta kuɗi, amma ace maganin bai ci ba? Kari ta ce,mu koma musu kawai gobe ke in abin ma ya ƙi wallahi sai mu nufi Nijar,zan binciko miki wani malami ko ince Boka.

Sun bar zancan a kan zasu koma in basu ga dai-dai ba,su nufi jamhuriyar Nijar, Allah ka tsare mu,Amin.

A’isha ko sam bata ma san hidimar da suke yi ba. Ranar ƙuƙewa ta yi tana ta ƙoƙarin yiwa Uncle ɗinta gurasa da miyar taushe. Ta haɗa zoɓonta mai daɗi, Uche ne ya taimaka mata ,Marka mai aiki taje ta sanar da Hajiya Jummai ta same ta suna magana da Karima,don haka ta sanar da su Suby cewa, amarya ta samu sake, tana can kitchen ta girka banza da wofi. Nan ko suka nufi kitchen ɗin suka shiga buɗe mata kuloli, suna cewa, me wannan ƙwamacalar wannan ƙazamiyar ƴar ƙauyen ta ke yi ne haka?” Aisha ko da kallo ta bisu, Sofy ta ce, ashe ma abincinsu ne irin na ƴan ƙauye. Suby ta ce,ke gaja wa kikayi wa wannan ƙwaɗon? Ita dai kallonsu take yi ranta yana zafi,ta ce ina ruwanku da kayana? Duk suka haɗa baki gurin cewa,sai mu zubar dashi,dube ta ƴar matsiyata kawai, A’isha ta ɗauki kulolin ta ta nufi ɗakinta ta dawo ta ƙwashe sauran kayan,su kam sai dariya suke yi mata,suna cewa in dai Alhaji ki kayi ma wannan ƙazantar ba ci zai yi ba ƴar neman gindin zama,zaki gane kuranki. Tagumi ta zuba tana zubar da hawaye,tuni ta kula waɗannan za su takura mata.

Yau tun huɗu Uncle ya dawo, domin tunda ya kira A’isha sau uku bata ɗauka ba,ya soma tunanin ko dai bata da lafiya ne? Ita ko sam bata ma san inda ta jefa wayar ba, kuma damuwar da take ciki bata tuna mata cewa tana da waya ba, domin dawowarta a jiya ne ma ta ɗauki wayar. Amma ba sa zuwa makaranta da waya. Lokacin da ya shigo tana wanka,zama ya yi yaga fitowarta, da ɗaurin ƙirji ta rufa da tawul ta ɗan yi yaƙe tare da kallon agogo tana faɗin, har ka dawo? Shi ko ita yake kallo yana son gano halin da take ciki,jin bai yi magana ba ne yasa ta maida kallonta gareshi ya ce “Beby me yake damunki?” Ta zauna bakin gado cikin irin murmushin takaicin nan,ta ce ba komai. Ya dawo kusa da ita wani guri yana miki ciwo ko? Ta ce “a’a,me ka gani ne Uncle?” Ya ce, “Sau uku ina kiran wayarki ba ki ɗaga ba, sannan yanzun na zo sai na same ki ba yanda ki ke ba.

A’isha baki kai lokacin da zaki haɗiye damuwa ba,sanar dani matsalar ki?” Ta girgiza kai “Yi haƙuri Uncle,ka bar zancan,maganar waya kuwa ni na ma manta ina da waya saboda ka san zaman makaranta yasa na saba da rashin waya.” Ya ce, “Ni fa Allah sai kin sanar da ni.” Ta ce, “to ni ban san me zan ce maka ba.” Ya ce, wani guri ne yake miki ciwo? Ta girgiza kai tare da cewa, a’a.

Kalli video

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More

Privacy & Cookies Policy