Bidiyo:- Rarara Ya Ba Ango Lukman Labarina Kyautar Mota

0

Rarara Ya Ba Ango Lukman Labarina Kyautar Mota

Rarara Yaba Ango Lukman LABARINA Kyautar Mota Da Wasu Kyautukan A Wajen Dinner Bikin Na Yusuf Sasen, Wato (Lukman Labarina)

Mawaki Rarara Yayi Wannan Bajintar Ne A Yayin Daya Halarci Taron Dinner Auren Jarumi Yusuf Sasen Da Ayi A Cikin Satin Nan. Inda Mawakin Yaba MC Da DJ, Kyautukan Naira Dubu Hamsin Hamsin.

Mawakin Ya Bayyana Cewa Zaiba Aisha Humaira, Wato (PA) Dinsa. Saqon Amarya. Inda Ango Zai Karbi Saqon Ta Hannunta, Inda Mahalarta Taron Ke Tunanin Itama Mota Zai Gwangwajeta Dashi.

Related Posts
1 of 405

A Lokacin Shagalin Bikin Ne. MC Yasa Wakar Sha’aban Sharada, Inda MC Ya Bukaci Mawaki Rarara Ya Bashi Kyautar Mashin Ko Mota, Nan Take Rarara Yace Bazai Mishi Karya Ba, Inda Ya Ba DJ Da MC. Kyautar Dubu Hamsin Hamsin.

Mawaki Rarara Dai Yakai Misalin Mintuna Biyu Da Wasu Daqiqa Yana Magana A Wajen Inda Yace Adaidai Lokacin Da Ake Bikin Yana Da Wani Meeting, Amma Haka Ya Tsallake Yazo Wajen Dinner

Daga Karshe Dai Yama Ango Da Amarya Fatan Alkairi, Inda Ya Musu Addu’ar Allah Yasanya Alkairi A Cikin Auratayyar Nasu, Ya Kuma Basu Zama Lafiya Amin Summa Amin.

 

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More

Privacy & Cookies Policy