Bidiyo Yadda Gobara Ta Kone Gidan Man NNPC A Birnin Dutse Jigawa 

0

Bidiyo Yadda Gobara Ta Kone Gidan Man NNPC A Birnin Dutse Jigawa

Bidiyo Yadda Gobara Ta Kone Gidan Man NNPC A Birnin Dutse Jigawa.

Kukaran ta wannan zai muku amfani.

Sasantawa Da Ƴan Adaidaita A Kano Amfanin Talakawa Ne.

DAGA Fadila H Aliyu Kurfi

Golden Pen 🖋

Ƙalubalen yajin aikin ƴan adaidai ta a kano

ni a mahanga ta idan gwamnati tace zata kalli yadda zata fidda haraji ko tawane hali a wurin matasan nan dake tuƙa baburan adaidai ta batare da kallon ƙuntatawa ko kimantawa gare su ba tofa tabbas hakan zai iya haifar da wasu ƙalubalen da zai iya sa al’umma cikin wani tashi hankalin.

Dama ga yadda yanayin tsaron kasar yake kamar “mai neman kuka ne bare an jefeshi da kashin awaki”.

Na duba ɓangarori kama haka.

1. Hukumar da alhakin karɓar harajin ta shafa tana yawan kalamai masu tunzurawa da nuna iko matuƙa ta kafafen gidan radio.

Ya kamata tayi bayanai da lafuzza masu tausasawa da jawo ra’ayi gasu matasan nan. Karbar haraji ba laifi bane tunda dashi ake manyan ayyuka da ƙananu.

Related Posts
1 of 405

2. Duba da yadda gwamnati ba zata iya samawa matasa ayyukan yi a kasa ba. Wadannan matasa sun dage matuƙa akan ganin sun kori zaman banza, shaye-shaye da sace-sace. A cikin wannan sana’a da suke yi, suna biyan.

– kuɗin makarantar kansu ko ƴaƴan su

– Kuɗin rashin lafiyar kansu ko ta iyalin su

– Sukan yi Aure da wannan sana’a

– Su biya kuɗin hayar gidajen su da duk sauran hidimomin su da suka shafi yau da kullum.

3.Shigowar ka Kano zaka iya gane cewa gwamnati bata yi tsarin da ya dace akan baburan adaidaita ba, saboda zaka iya cin karo da yaro dan shekara 15 ko 16 ya hau adaidaita yana tuƙawa wanda duk mai hankali yasan irin waɗannan yara basu gama mallakar hankalin kansu ba balle susan kiyaye dokar tuƙi ko ƙa’idojin shi.

Kuma irin waɗannan yaran ne in ka yi rashin sa’a suka goga maka ko ka goga masu zaka rikajin furuci marar daɗi daga bakunan su, kuma duk girman shekarunka basa dubawa zaka ga wani ka haife shi wani kama yi jika da shi.

Kunga wannan ma abun dubawane. Sannan ga rashin bin ƙa’ida ga wasun su, zasu iya tare hanya don ɗaukar fasinja ko kaga sunyi tsaye akan titi ajiye fasinja. Ya kamata suma su sa adalci akan tuƙin su sannan su samar da ƙungiyoyi wadda za su riƙa bibiyar yadda suke tuƙi wadda zata riƙa shiri a gidajen radio na wayar da kansu yadda za su yi mu’amula tsakanin su da tsakanin su da fasinja dama jama’a baki daya.

4. Zaka samu adaidaita tun daga biyu zuwa ukku suna amfani da lamba ɗaya, hakan sakaci ne daga mahukunta ko ƙaramin yaron da bai gama mallakar hankalin kansa ba yana tuƙin adaidaita.

Kamata yayi ayi lasisin tuƙi kamar yadda masu mota suke dashi, lasisin ya kasane yana ɗauke da duk wani bayanan da suka shafi mutum ta yadda za’a kare ka’idoji da sharuɗɗan tuki da kore ƙananan yara masu tuƙa adaidaita akan titi. Sannan ayi takardun lamba sahihai wadanda ke ɗauke da duk wasu bayanai na nuna mashin din mallakin wane ne. Kuma a tsananta duba lasisin tuƙi da takarsun adaidaitan do karesu daga sharrin sacewa ko ɓata. Indai ansa adalci an fidda halin mu na cin hanci insha Allahu.

5. Idan akace za’a yi kuskuren hana adaidaita matsalolin tsaron da aka ga an samu nasarar su a jihar kano zata tsananta domin akalla za’a iya samun matashi da magidantar da ke tuƙi adaidaita akalla miliyan ɗaya banda ma mutanen dake karkashin su bani da adadin kididdigar na yi hasashe ne kawai to yanzu ace yau an daina adiadaita lallai ɓalle shaguna, ƙwacen waya, fyade, haurawa gidajen mutane, shiga gurbatattun ƙungiyoyi, satar mutane, shiga kungiyoyin ƴanta’adda zai yawaita. Mahukuntan sunyi sama ta yadda wannan ba zai shafe su kai tsaye ba, amma matsakaita dana ƙasa su wannan bala’in zai shafa.

Saboda haka ya kama asamu maslaha da daidaito a tsakani.

Allah kaba jahohin mu zaman lafiya da ƙasa ta Najeriya dama Duniya baki ɗaya. Allah ka fidda mana son zuc‍iya kasa mana son junan mu Ameen.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More

Privacy & Cookies Policy