Bidiyon Yadda ake hukunta abduljabbaru kafin ayi masa babban hukunci

0

Bidiyon Yadda ake hukunta abduljabbaru kafin ayi masa babban hukunci

Bidiyon Yadda ake hukunta abduljabbaru kafin ayi masa babban hukunci

Na yarda Mallam Abduljabbar ya yí Mãnyan laifúka gúda huɗu – Áliyu Ɗahíru Aliyú.

1. Ya yí fada da Salafíyya.

2. Ya yí fada da yan haqíqa.

3. Ya yi fada da wasú yan Qadiríyya

4. Ya yí fada da wasú yan síyasa.

Wadannan sú súka hadu súka mayar da fadansu céwa na zagín Annabí (saw) né alhalin su kansu sun san karya suke.

Nì daí da Annabi (saw) ya yí arahar da zan yì siyasa da shi, gwara a yau rayuwata ta fi. Anya wasu sun yarda idan an mutu za a tashi kuwa?

Na yi imani bayan wannan rayuwar akwai wata rayuwar mafi muhimmanci da adalci. Ta yaya zan iya kallo Annabi (saw) a ranar alkiyama tare da na san na yi amfani da shi a duniya wajen bukatuna?

Related Posts
1 of 408


Zan iya mutuwa a yanzu-yanzu ko an jima. Ko wani bai kasheni ba, zan mutu a gida ko asibiti. Daga karshe dai duk mutuwa zamu yi ko mun shirya ko bamu shirya ba, kuma babban abin da zamu tarar shi ne abin da muka kudirta ko muka aikata.

Fatana Ubangiji Ta’ala ya sa duk rintsi ya haneni siyasantar da addini ko karfafa masalahar duniyata fiye da ta lahirata. Ubangiji kada ka bari rashin tsoronka ya sa mu aikata zalinci da sunanka ko mu goyi bayan zaluncí da súnanka.

ماذا تقول

Mé za kúce ?

DA ƊUMI-ƊUMI: Kotu a Kano ta yanke wa Abduljabbar hukuncin kisa.

Wata Kotun Shari’ar Musulunci da ke zamanta a Kofar Kudu a Jihar Kano, karkashin jagorancin Ibrahim Sarki Yola, a yau Alhamis ta yanke hukuncin kisa ta hanyar rataya ga malamin addinin Musulunci, Sheikh Abduljabbar Kabara.

Daily Nigerian Hausa ta ruwaito cewa an maka Kabara a kotu ne bisa wasu kalamai na batanci ga Annabi Muhammad (SAW) a wajen karaturruka sa.

Da yake yanke hukuncin, Sarki-Yola ya gamsu da dukkan shaidun da lauyoyin masu gabatar da kara suka gabatar, tare da cewa sun tabbatar da gaskiyarsu ba tare da wata shakka ba.

“Na tabbata cewa lauyoyin masu gabatar da kara sun yi nasu bangaren kuma sun tabbatar da hujjojinsu ba tare da wata shakka ba,” in ji Sarki-Yola.

Jaridar Daily Nigerian Hausa ta ruwaito cewa an shafe watanni goma sha biyar ana shari’ar kafin a yankewa malamin hukunci a yau Alhamis.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More

Privacy & Cookies Policy