Bidiyon Yadda Saurayi Ya Samu Damar Sumbatar Budurwa
Kalli Bidiyon Saurayi Da Budurwa Suna
Sumbatar Juna Ba Kunya Ba Tsoron Alla
MATSALAR TSADAR AURE DA LALACEWAR TARBIYAR MATASA A AREWA — Maiwada Dammallam
Na fahimci gagarumin kokarin Karamar Hukumar Gumel ta Jihar Jigawa na sauk’ak’a ma matasa lamurran aure. Tare da haka kuma na hangi babban gib’i a cikin k’udurin wanda zai hana karb’uwar wannan namijin kokarin bisa dalilai kamar haka.
Tsadar aure a Arewa takobi ne mai kaifi biyu. Duka b’angarorin biyu suna gasa ma kansu gyad’a a hannu kafin su cinma burinsu na k’ulla auratayya. B’angaren saurayi sai sunyi ma kansu k’ark’af wajen k’ok’arin had’a lefe mai kwatankwacin darajar da suke auna kansu a idon jama’a. B’angaren budurwa kuma zasu maida biki ta hanyar yi ma kansu k’ark’af wajen yi ma amarya kayan d’aki daidai da darajar da suke auna d’iyar su kuma mafi yawancin lokaci suna himmatawu wajen ganin sunyi kayan d’aki da zasu yi daidai da na budurwar da aka aka kaima ma d’iyar su.
Sai gashi kaf cikin k’udirin babu inda aka kalli d’awainiyar da iyayen yarinya ke yi kama daga kayan d’aki zuwa kayan gara na abinci da suke lafta ma angon da y’an awoyi k’adan a baya waliyan shi suka yi alk’awarin a madadin shi cewa ya d’auke ma iyayen yarinya nauyin ci, sha tufatarwa da muhallin ta. Kenan, mawallafan wannan k’udiri ko dai sun manta iyayen yarinya na yi ma d’iyarsu kayan d’aki ko kuma basu fahimci irin kayan d’akin da akeyi ba a wannan zamani da ango gudummuwar bangaye, fenti da rufin kwano kawai yake bayarwa a inda iyayen amarya su zasu samar da duk wani abu na cikin gidan kama daga gadaje (dan yanzu abin kunya ne akai gado d’aya), kujeru, kayan alatu har zuwa kofin shan ruwa da za ayi amfani dasu a cikin gidan. Kenan, an yi tuya an manta ba da albasa ba kawai har da man tuyar.
Matsalar k’udirin ta biyu itace cewa yadda linzami yafi k’arfin bakin kaza haka gyaran wannan matsalar yafi k’arfin Karamar Hukuma. Yau idan Karamar Hukumar Gumel ta d’auki matakin hana yin lefe a Gumel, shin tana iya hana ma’aurata tsallakawa mak’wabtun Kananan Hukumomi su kai lefe, su amshi kayan d’aki a d’aura auren sannan su zubo a mota su maido cikin Gumel a matsayin y’an gida da suka dawo daga balaguro. Idan aka kalli lamarin ta wannan mahangar, kenan an k’ara ma yin aure wahala ne maimakon a rage.
K’ad’an daga cikin kyawawan siffofin doka shine ayi wadda za’a iya tilascin bin ta kuma ta zama wadda za tayi adalci ga duk wanda ta shafa. Wannan doka Idan har an yi ta yadda take a k’udirin ba za tayi ma b’angaren amarya adalci kuma Karamar Hukumar Gumel bata da karfin tilasta abi ta. Kenan, za ta zama abin dariya da raunana k’arfin ikon Karamar Hukumar.
Shawara itace, Karamar Hukumar Gumel ta m’ika hannun k’awance ga sauran Kananan Hukumomin na Jihar Jigawa don su tunkari Gwamnatin Jihar Jigawa da buk’atar wanzar da doka ta bai d’aya a Jihar Jigawa wadda zata kalli lamarin daga duka b’angarorin don kawo gyara. Yin haka zai yi maganin ma’aurata su rik’a hijira daga wannan Karamar Hukuma zuwa wata don yin irin auren da suke jin shine daidai da su ba wanda yayi daidai da hankali ba.
A tare da haka akwai muhimmayar b’ukatar Shugabannin iko da na addini su zage damtse wajen wayar ma al’umma da kai akan irin hatsarin dake tattare da tsawallawa a cikin harkar aure. Musulunci ya tanadi ayi ma yarinya aure da ta balaga ba don bai so d’iya ta zauna wurin iyayen ta bane. Ya tanadi haka ne don yasan takai inda zata iya sha’awar namiji har ta takura Idan abin yayi tsanani. Ba abin kace-nace bane fahimtar cewa tsananin takura yana iya tilasta ma baligi ko baliga wurgar da duk wata tarbiya dan warware matsalar rad’adin buk’atar zuciya. Akan haka muslinci ya tanadi a aurar dasu da sun kai wannan gab’ar kafin su afka ma fitinar sha’awa da Kalangun Shaid’an.
Kenan, Idan ka k’i aurar da baligar da ta kai wannan zangon don jiran sai ka samu mai k’arfin da zai kawo lefe na fitar tsara, to tabbas ka hau layin da d’iyar ka zata aurar da kanta a bisa kud’i k’alilan ba tare da biki ko g’uda ba. Haka kuma, Idan ba ka taimaka ka sauk’ak’a ma samari balagai yin aure ba, to suna nan a matsayin dawwamammar barazana akan d’iyar ka. Abin fahimta a nan, shine daga mai mata d’aya har zuwa mai 4, sun fi kowa sikelin auna rad’adin sha’awar zuciya. Kenan, akwai yaudarar kai mutum ya r’ika tunanin baligin d’an shi ko d’iyar shi su suna da wata mafita kan wannan tsarin na rayuwa sab’anin wanda shi ya dogara akai.
Tare da haka kuma akwai sauk’ak’awa da kimiyi ta zamani ta kawo. Hanyoyi huld’ayya tsakanin Matasa na zamani sun yawaita ta inda har bai yiwuwa iyaye su sa ido kan tarbiyar ya’yan su don gudun kada ta gurb’ata. Kama daga Facebook, Whatsapp, Instagram da ire-iren su, duka hanyoyi ne da matasa ke huldayya da juna tun daga ta arziki har ta tsiya. D’iyar ka na zaune gaban ka, sai tayi awoyi tana batsala da wani a gabanka ba tare da ka sani ba. Mafi yawancin iyaye ma su ke sayen “data” da ya’yan su ke shiga yanar gizo.
To yakamata mu fahimci cewa “yanar Gizon” nan fa da gaske tarko ce Kamar yanar gizon da aka sani. Yanzu an wuce zamanin da zaka zauna bakin zaure ka hana d’an aike shiga gidanka don kiran d’iyar ka. Zamani wanda d’an aiken ta gabanka zai wuce ya shiga d’akin d’iyar ka ya kai mata sak’on lalata. Fad’akarwa da ilmantar da mutane game da wannan babbar matsalar yana daga cikin gagarumin aikin da ke kan mahukunta don fahimtar inda ake da inda aka dosa.
Da dad’i jin yadda Hausawa ke cewa, Ko cikin tandu akwai gabas. Yanzu kam tabbas muna cikin tandu kuma ya wajaba mu tattara hankali wuri guda don gane gabas mu samu mafita. Ya wajaba mu taimaki ya’yan mu ta hanyar kare su daga fad’awa cikin masifa ta hanyar bud’a masu hanya mafi sauk’i ta kare mutuncin su da namu. Abin murna ne da Karamar Hukumar Gumel har ta fahimci akwai wannan matsalar sab’anin biris da matsalar da gwamnatocin Arewa suka yi har aka kawo inda yake. Babban mataki na warware matsala shine yadda da cewa akwai matsalar. To zan so gwamnatocin Arewa su kalli wannan matsalar da ido d’aya, kallo na natsuwa irin na wanda ke cikin tandu yana neman mafita.
Allah Ya bada ikon yin hakan, Ya kuma bada nasarar abin Idan anyi.