Bikin Halima Atete ya nuna tasirin jarumar a Kannywood

0

Bikin Halima Atete ya nuna tasirin jarumar a Kannywood - Kannywood - News, reviews and more › hausa

Wata magana mai daɗi: Amarya Halima da ango Mohammed a wajen dina

BIKIN auren Halima Yusuf shaida ce ta irin tasirin da jarumar ta ke da shi a Kannywood, a lurar da mujallar Fim ta yi.

An ga hakan ne kuwa ta hanyar yadda manyan jarumai da mawaƙa daga industiri su ka kwamba a Maiduguri, babban birnin Jihar Borno, domin yi mata kara.

A irin wannan mawuyacin lokacin, ba kowa ba ne zai niƙi gari ya tafi Maiduguri biki im babu danƙon zumunci a ciki. Halima ta yi zaman lafiya da kowa a Kannywood, kuma ita mai faɗa a ji ce, don haka ‘yan fim su ka yi mata kara sosai.

Amarsu ta ango: Halima Atete

A jiya Asabar, 26 ga Nuwamba, 2022 ne aka ɗaura auren jarumar da mijin ta, Mohammed Mohammed Kala.

Mujallar Fim ta gano cewa shi dai angon, ɗan siyasa ne wanda ya taɓa zama mataimaki na musamman na Sanata Ali Ndume. Yanzu babban ma’aikaci ne a Hukumar Raya Muradun Ƙarni ta Ƙasa.

Related Posts
1 of 408


Bayan ɗaurin auren, an yi ƙasaitacciyar dina inda jarumai mata su ka yi shiga ta kece raini tare da ƙure adaka. Sun haɗa da Hadiza Gabon, Momee Gombe, Jamila Nagudu, Samira Ahmad, Fauziyya Maikyau, Sadiya Gyale, Hadiza Kabara, Fati Yola, Fati Bararoji, da Teema Makamashi.

Ita kuwa amaryar, bakin ta ya ƙi rufuwa saboda murna.

Fitattun mawaƙa sun gwangwaje sosai. Ado Gwanja ya baje kolin sa, yayin da Adam A. Zango, wanda ya je a matsayin jarumi, ya rikiɗe zuwa mawaƙi.

Shi ma mai gabatar da biki, M.C. Ibrahim Sharukan, ya gwangwaje son ran sa.

Amarya da ‘yan matan amarya daga Kannywood

Haka su ma maza, akwai tawagar Abdul Amart sai sauran jarumai da furodusoshi da su ka haɗa da Usman Mu’azu, Baballe Hayatu, da Baffa Ahmad.

Amarya Halima dai ta tare a gidan mijin ta da ke wata unguwa da ke kusa da Barikin Sojoji a Maiduguri.

Daga hagu: Fati Yola, Teema Makamashi, Jamila Nagudu da Hadiza Kabara
Amarya da ango

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More

Privacy & Cookies Policy