Darakta Ibrahim El-Mu’azzam ya zama angon Maryam
Ango Ibrahim da amarya Maryam cike da farin ciki
A JIYA Lahadi, 25 ga Disamba, 2022 aka ɗaura auren darakta a Ibrahim El-Mu’azzam da amaryar sa Maryam Alhassan.
An ɗaura auren a unguwar Kabara da ke cikin Birnin Kano da misalin ƙarfe 11 na safe, kuma ‘yan fim da dama sun halarta.
Ibrahim El-Mu’azzam da Maryam Alhassan
Tun kafin ranar dai angon ya shirya taron shagalin biki na musamman wanda jama’a da dama su ka halarta.
Tuni dai amarya ta tare a ɗakin ta.
Da fatan Allah ya ba da zaman lafiya da fahimtar juna.
Sun zama ɗaya: Ibrahim da Maryam
Ango Ibrahim El-Mu’azzam da amaryar sa Maryam a wurin bikin auren su.