Edita a Kannywood, Yakubu Hafizu Ɗandago ya zama angon Safiyya – Kannywood – News, reviews and more › hausa
Ango Yakubu da amarya Safiyya a tsakiyar abokan arziki a wajen walimar auren su
A DAIDAI lokacin da ake murnar shiga sabuwar shekara, shi kuma editan finafinai a Kannywood, Yakubu Hafizu Ɗandago, wanda aka fi sani da Malam Alhaji Edita, angwancewa ya yi da sahibar sa, Safiyya Sa’eed Mika’iku.
A ranar Lahadi, 1 ga Janairu, 2023 aka ɗaura auren su a Masallacin D.O. da ke Gwale a cikin Birnin Kano da misalin 11 na safe.
‘Yan fim da dama sun halarci ɗaurin auren.
Yakubu Hafizu Ɗandago da amarya Safiyya Sa’eed Mika’ilu
Tun kafin ranar ɗaurin auren an yi shagalin biki a ranar Asabar a Hazeen Events Centre da ke Farm Centre.
Allah ya ba da zaman lafiya da fahimtar juna.