Falalu Dorayi Ya Mayar Da Martani Ga Afakalla Kan Hana Adam A Zango Shiga Kano

0
IMG 20200217 173453 052

Yanzu Shafin www.PressHausa.com Ya Samu Labarin Cewa Daya Daga Cikin Daraktocin Masana’antar Kannywood Falalu Dorayi Ya Mayar Da Martani Kan Hana Adam A Zango Shiga Kano, Wanda Hakan Ya Biyo Bayane Ta Indah Shugaban Tace Fina-Finnan Hausa Afakallah Ya Gindiya Dokar Ga Jarumi Adam A Zango.

Ga Dai Abinda Daraktan “Falalu Dorayi” Yake Cewa:-

(” Daga falalu_a_dorayi – ADALCI
Idan har hukuma zata bawa film certificate a nuna shi a Cinema, duk da akwai Jarumai marasa register da hukuma a shirin, babu hujja hana jaruman cikin film zuwa su gana da fans dinsu. Idan akwai hujjar, zata fara ne daga lokacin da Film din yazo hannun hukumar, sai su hana certificate su ce wane bai register damu ba.

Abin da mamaki, nasan Jarumai da mawaka da dama da basu da lasisin hukumar suna halattar gurin nuna film a Filmhouse, wani film sune a ciki, wani kuma kallo kawai suka je, ba’a taba yinkurin kama su ba, sai rana tsaka ace an hana wani saboda bashi da lasisin hukuma.

Adalci shine ayi hukunci na bai daya babu nuna fifiko, menene bambancin sa da DIJA? Ba a kano take ba, ba a kano yake ba, idan har za’a barta tazo mai zai hana zango zuwa? Bana jin DIJA na da lasisin hukumar. Haka kuma Idan za’a bar wadancan Jarumai da mawaka marasa lasisin hukuma su zo kallo, Mai yasa aka hana zango?

Related Posts
1 of 405

Kungiya raayi ce, idan kaga abin da kungiya take baya gamsar da kai, kana da ikon fita, kuma ba kan zango aka fara fita daga kungiya ba. Adam A. Zango ya sanar ya fita daga kungiya, amma ba shine yake nuna ya daina  zamunci da Kano ba. Mai yasa hukuma take kokarin mai da abin ya zama hada husuma, ni dai ban taba ji zango ya zagi ko cin zarafin kano ba. Kar muyi amfani da siyasa mu jefi Yan uwanmu da sharri.

Jagora nagari ana so niyyarsa ta zamo mai kyau bata san zuciya ba.
Sannan ya zamo mai yin abu domin Allah, ba domin a gani a fada ba. Kuma kar ya zamo mai aibata ko cin zarafin mutane.

Idan Jagora yana so wadanda yake jagoranta suyi masa biyayya, sai yai Jagoranci da adalci. Ya kiyaye nuna fifiko. Ya bawa dokar gaskiya dama tai aiki, ba dokar fadi a baki ba.

Jagora ya zamo mai aiki da  mashawarta nagari, kar ya zamo mai mulki domin bukatar wasu, hakan shike kawo mulkin zalinci, har ta kai ana kin girmama juna.

Tunatarwa
Qurani a cikin An-Nisa’i (58)
Allahu (SWT) Yace;
“Lallai ne Allah yana umarnin ku bayar da amanoni zuwa ga masu su.
KUMA IDAN ZAKU YI HUKUNCI TSAKANIN MUTANE, KUYI HUKUNCI DA ADALCI, LALLAI NE ALLAH MADALLA DA ABIN DA YAKE YI MUKU WA’AZI DA SHI.
LALLAI NE ALLAH YA KASANCE MAI JI NE, MAI GANI.”

Ku Tura Zuwa Facebook, WhatsApp, Twitter, Da Dai Sauran Social Media Platform. Kuci Gaba Da Kasancewa Taredamu A Koda Yaushe Domin Samun Labaran Kannywood Da Labaran Duniya Baki Daya.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More

Privacy & Cookies Policy