Fati Ladan Ta Cika Shekaru 9 A Dakin Mijinta
Tsohuwar Jarumar A Masana’antar KannyWood, Fati Ladan Ta Cika Shekaru Tara (9) Cif Cif A Dakin Mijinta Shetima. Jarumar Dai Tayi Aurenta Ne A Shekarar 2013, Inda Tunda Jarumar Tayi Aure Tayi Bankwana Da Masana’antar Ta Kannywood.
Allah Ya Albarkaceta Da Haihuwa Yara Biyu Zuwa Uku. Inda Suke Zaune Zaman Lafiya Da Angon Nata.
Kafin Fati Ladan Din Tayi Aure, Jaruma Ce Da Taja Ragamar Manya Manyan Fina Finan KannyWood, Wanda A Wancan Lokacin Tauraruwarta Tana Haskakawa Sosai.