Gargadi Da Jankunne Gameda Abinda Ya Faru Da Maryam Booth (” Kyara Kayak Ka….? “)

Da bidiyo ko hoton tsiraici na Maryam Booth ya fito, abinda na fara yi shine rokon wasu da su cire sannan su daina rabawa, tabbas na yi kima a idanuwansu sun saurare ni.
Abu na biyu da na dau niyyar yi shine na yi rubutu na musamman kamar yadda na yi lokacin Maryam Hiyana a jaridar Leadership ta turanci inda na jawo hankali mutane irin hadari da ke cikin kallo ko raba hotunan tsiranci.
Allah Ya taimake ni da yawa sun saurare ni daga amsoshin texts da na samu daga jama’a da dama.
Na kuma bi wannan ra’ayina da special report watau rahoto na musamman inda na yi hira da lauyoyi, iyaye da ‘yan mata. Allah Ya taimake mu wannan zance ya mutu sai dai a kan tuna ne in abu irin haka ya taso.
Na Maryam Booth ban so in ce uffan ba ganin yadda na ga mutane da yawa suke ta rubuta abinda ni ke niyyar rubutawa na Allah wadai ga rarraba irin wannan hotuna inda wasu ma suka mata uzurin cewa kila kawarta ce mace ta dauke ta yayin fitowa wanka.
Na baru ne don martani da ita Maryam Booth ta bayar amma kafin in zo ga Maryam, zan zo gare mu duka da mu ji fa tsoron Allah, in har ma ba za mu ji tsoronSa ba to mu ji na bala’i da ke tattare da yada irin wannan alfasha.
Ya kamata a ce saboda tausayi da imani muna tsoron ganin tsiranci wani ko gawar wani ko wata amma abin mamaki yanzun da su muke kwalliya a bangunan kafafen sada zumuntarmu.
Ya kamata jama’a mu tuhumi kanmu a yayin da jini, gawanwaki da tsiranci dan Adam dan’uwanmu ya daina ba mu tsoron da jimami, ya hana mu barci, lalle wannan yana tartare ne da rashin imani da tsoron Allah.
In haka yana faruwa cikin al’umma kuma ba mu cikin kuka da jimami tabbas rayuwarmu ta kasance irin ta dabbobi kuma abubbuwa da dabbobi ke yi shi za mu wayi gari muna yi wanda tuntuni ma an fara.
Na fada a da, zan sake fada, dukanmu masu laifi ne amma wani in ya yi zai yi kuka ya shiga damuwa ko da kuwa zai kuma yi wanda a lokacin na ce ta yiwu Maryam Hiyana ‘yar Aljanna ce kuma Allah na sonta ya sa aka gane ta don ta tuba kuma masu kallon tsirancinta su kwashi mata alhakin da ta kwasa da wadanda za ta kwasa nan gaba.
Tabbas an ce Maryam Hiyana ta some da wannan bidiyo ya fito bayan komai ya lafa sai aurenta muka ji da har yau ba a sake jinta ba sai dai in ta haihu a fada mana.
Kila a cikin wadanda suke ci mata mutunci har yanzun wani yana aikata assha, asirinsa lif ya ke yana jin dadi ya fi ta!.
Madalla, ina masu bai wa Maryam Booth shawara? Wa ya ce ta fito fili ta yi magana? Na ta bai ma lalace kamar na takwararta ba da aka ga namiji aka ji muryarsa. Mutane sun mata uziri fiye da kowa a baya amma sai ga shi ta fito da kanta tana namiji ne ya dauke ta! Na so da ta yi shiru sai dai mu ji tana kuka, ta shiga yanayin dimuwa amma duk wanda ya ba ta shawarar ta yi magana bai kyauta ba ko ba ta kyauta wa kanta ba.
In kun lura wannan irin bala’in da muka shiga kenan, muna ado da sabawa Allah, tsiranci, jini da gawawwaki ba su da tasiri a zukatanmu. Na ji wata ma an ce ta ce, in ta bushi iska, za a ganta ta fito tsirara watarana! Subhanallah! Kun ga irin hali da muka shiga ko? Mun daina tausaya was kanmu balle junanmu sannan muna ta tambaye mai ya sa bala’i ke faruwa da mu bayan mu ke jawowa kanmu.
A duk lokacin da muka cire wa kanmu kunya, tsoron, tausayi da jimami, Wallahi komai ma za mu iya yi a tsakaninmu.
A cikinmu babu wanda ba ya sabawa UbangijinSa amma in sabo ya zama abun ado a tsakaninmu, to tabbas al’umma ta shiga uku!.
Allah Ya shirye mu da zuriyarmu bakidaya, Ya fidda mu kunyar duniya da ta kiyama.
Daga Mairo Muhammad Mudi.