Haka Zasu Barmu”,Yadda Zainab Indomie da Mama Daso suka Tiƙi rawa A TikTok
Wani fefen bidiyo da Jarumar Kannywood wadda taga jiya kuma taga yau,Saratu Gidado wato wadda akafi sani da Daso.
Jarumar ta wallafa wani fefen bidiyon dakiku a shafinta na Tiktok sanye da wakar Warr ta Ado Gwanja tare da Zainab Indomie.
Yanayin yadda sukayi rawar yayi matukar nishdantar da masoyan nasu,domin sun casu iya casuwa a wakar ta Limamin Mata (Ado Gwanja).
Zainab Indomie ,idan baku manta ba tana daya daga cikin manyan Jaruman Kannywood da sukayi tashe kamar babu gobe,domin a lokacin ta ba’a maganar wasu su Rahama Sadau,Gabon balle kuma Nafisat Abdullahi.
Nasan kun gaji da karantawa,ba tare da bata lokaci ba zaku iya kallon cikakken bidiyon anan kasa, kuci gaba da kasancewa damu domin samun labarai da dumidumin su.