Hotuna: Bikin auren jaruma Halima Atete da Mohammed
Halima Yusuf Atete cike da murna a wajen dinar auren ta
LALLAI an sha biki. Amarya da angon ta da ‘yan matan amarya sun ƙure adaka.
Rabon da a ga bikin aure irin na jarumar Kannywood Halima Atete an daɗe.
Amarya Halima Atete
Jiya Asabar, 26 ga Nuwamba, 2022 aka ɗaura auren Halima da Mohammed Mohammed Kala a Maiduguri.
Ga wasu hotuna na bikin, musamman dinar da aka yi a jiya, mujallar Fim ta kawo maku domin ku kashe kwarkwatar ido.
MC Ibrahim Sharukan ya na gabatar da amarya
Daga dama: Maryam Ceeter, Fauziyya Maikyau, Sadiya Gyale da Samira Ahmad
Momee Gombe
Baballe Hayatu tare da Sadiya Gyale
Samira Ahmad ta na yi wa amarya liƙi
Daga hagu: Maryam Ceetar, Samira Ahmad, Fati Yola, Fauziyya Maikyau da amarya Halima Atete
Amarya Halima Yusuf Atete
“To, masoya, sai wata rana. Ni na tafi ɗakin aure!”