Idan har wanda zan aura talakane to gwara na cigaba da zama haka har na mutu

0

A cewar wata budurwa~ Idan har wanda zan aura talakane to gwara na cigaba da zama haka har na mutu banyi aure ba Turƙashi.

Wata Matashiyar budurwa mai suna Fatima Sheka ta jawo cece-Kuce tare da tayar da jijiyoyin wuya ga samari inda ta yi wata magana wacce samari basa son jin irinta. 

Matashiyar ta bayyana cewa;

“Nifa inhar talaka zan aura to gara na mutu banyi auren ba.”

Tun bayan wallafa rubutun a shafinta na Twitter sama da mutane dubu 1 ne suka bayyana ra’ayoyinsu akan kalaman Maryam, inda da yawa daga cikin masu mayar da martani suke tofin ala tsine akan furucin da ta yi.

Ga wasu daga cikin tsokaci da wasu suka yi a kasan rubutun kamar haka.

Fauzeeybash

I dunno how u ppl come up with this kind of nonsense, but wallahi kiji tsoron ranar da Allah zai kamaki da gatsenki.

Zinariya

Related Posts
1 of 407


Subahanallahi baby fadi alheri ko kiyi shiru 😎

Abduljalal

Wallahi kin burgeni karki yarda ki auri talaka, kijira har sai mai kudi yazo zaki iya kai har shekara 65 kafin kiyi aure

Muhammad

Wa-iyazubillahi! To Allah ya baki mai kudi kuma ya hanaki kwanciyar hankali.

Eng.

Gaskiya Fatima bakida ilimin addini, to kudi mutum shi yake ba kanshi? Sai ki auri mai kudin, kuma ki samu ashe kashin tsiya ne dashi sai kun yi auren ku talauce sai yaya Kenan?

Wannan kadan Kenan daga cikin ra’ayoyin da mutane suke ta bayyanawa a kasan rubutun da Fatima Sheka ta yi. Shin ku menene naku ra’ayin?

To jama’a zamuso mukarɓi ra’ayoyin akan wannan lamari don jin tabakinku zamuso kubiyomu kaitsaye tasahinmu na tsokaci kaitsaye.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More

Privacy & Cookies Policy