Innalillahi Gaskiya Wannan Ba Tarbiyya hausawa Bace Kalli Yadda Amarya Take Rawar Iskanci Agaban Kowa
Innalillahi Gaskiya Wannan Ba Tarbiyya hausawa Bace Kalli Yadda Amarya Take Rawar Iskanci Agaban Kowa
YADUWAR ZINA ACIKIN AL’UMMAH.
Wasu daga cikin dalilan da suka sa wannan bala’i ta zina ta yawaita cikin AL’UMMAH.
1. TALLE: Mafiya yawan yara matan dake yawon talle a cikin kasuwanni, Garejoji, Tashoshin mota, da Unguwanni suna cikin hatsarin afkawa cikin wannan mummunar
dabi’a. Ba don komai ba sai saboda yadda kullum zasu rika jin kalamai na batsa da kuma miyagun wasanni irin na batsa da suke samu daga shashashun samari da kuma tsofaffin yan tasha.
2. WAYOYIN SALULA: Wayoyin salula suna taka mummunar rawa cikin yaduwar fasadi da lalacewar tarbiyar AL’UMMAH. Musamman ta bangaren HOTUNA da VIDIYO NA BATSA da recording na kalmomin batsa wanda matasa maza da mata suke turawa a wayoyinsu. Yara Qanana sukan kalli hotunan yadda ake jima’i. Daga nan kuma sai shedanci ya shiga zukatansu su fara tunanin hanyoyin da zasu bi su rika samun biyan bukatarsu, alhali da can irin wannan tunanin bai taba shiga kwakwalwarsu ba.
YADUWAR FINAFINAI: Yaduwar Finafinaina waje da kuma na gida shima ya taimaka wajen watsewar al’amura. Ba don komai ba, idan ka lura da yadda rayuwar Matan hausawa take acikin shekarun 1980 zuwa 2000 zaka ga ba daidai take da wacce mukeyi yanzu ba.
Tun daga salon dinkuna da suke sawa, da kuma yadda suke kula da tarbiyar yaransu, da kuma tarbiyarsu ga mazajen aurensu.
WURAREN PARTY: idan akayi la’akari da yadda kullum harkokin party suke kara bunkasa a tsakanin matasa da kuma irin watsewar da akeyi awajen, lallai za’a fahimci cewar harkar party tana daga miyagun Abubuwan dake addabar tarbiyar al’umma. Ana haduwa maza da mata awajen kuma ana aikata haramtattun abubuwa iri-iri wadanda ba sai na lissafa ba.
DON HAKA ya zama wajibi a matsayin ka/ki na uwa da uba Ku tsaya tsayin daka wajen lurada tarbiyar yaranku, domin ALLAHU SWT cewa yayi “Ku kare kawunanku da na iyalanku daga shiga wuta” wallahi ALLAH zai tsaida kai ya tambaye ka ya ka tafiyar da amanar da ya baka? Kuma sai ka amsa.
ALLAH ya shiryar da zuri’ar musulmai baki daya.
ZAUREN AHLUL SUNNAH
Tabbas , mutumen arewa yajikunƴa musamman matasa da sarakuna da malammai, amma attajirai suna ƙo ƙarie” amma mafi munin lalacewa sune ƴansiyasar arewa, da ƴan bokon arewa ,da ƴa ƴan sarakunan arewa,
Don wallahi su suka lalata arewa su sukaci amanar arewa, su suka lalata arzikin arewa
Kuma su suka sace kudin arewa , kuma su suka haddasa bala’inda kefaruwa arewa,
Da hannusu wajen lalacewar tarbiyar ƴan arewa, da hannunsu wajen ƙirƙiro ƴan daba masu kashe musu waɗanda basa so,
Da hannunsu wajen shigowa da ƙwaya ,
Da hannunsu wajen shigo da makami
Da hannusu wajen lalata ƴam matan talakawa
Da hannun su wajen lalata sharia,
Da hannunsu wajen taɓar ɓarewar al adun mu
Nagado , daga aure har yadda zaa yi soyayya
Da hannunsu jen taɓar ɓarewar ilimi
Da hannunsu wajen shiuka ƙiyaya wa jiuna sabo da siyasa
Wannan kadan daga cikin abida yakkawu ma
Arewa lalaci da karewar tattalin arziki.
A arewa ba haushe ke kawuma bafulatani
Bindiga don yaje yakashe yan uwasa hausawa
Saboda kuɗi ko siyassa,
A arewa zakaga bafulatani yaje ya kore shanun dan uwansa bafulatani ya kaiwa bahaushe
Ya sayar yasammai wani abu daga ciki,
A arewa maƙwabci zai yiwa macce asihhiri don ya aureta ko fasikanci kuma da sunan musulumci, kuma da sunan malanta
A arewa zakga musulmi ya aje matsafi don yabashi kariya sam ya matta da ubangijin da yahhalicceshi
Ya allh ka sauƙa ƙemuna abubuwanda suka addabe mu ,, ya allh kasa sugane kuma kabasu iekon tuba zuwa gareka
Ya allah ka tsarkake zukatanmu ya allah kashirda mu kahanamu shig ɓata
Kanuna muna daidai kabamu iekon yin dai dai