Jaruma Rashida Mai Sa’a Ta Koka Kanrashin Aure, Daya Daga Cikin Jaruman Kannywood

Shafin Pressloadedng Yau Munah Dauke Da Labarin Wata Jaruma A Masana’antar Kannywood.
Babban burin kowacce mace a rayuwa shine da ta kai minzalin aure ta samu miji ta yi aure abinta.
Yayin da ake yiwa jaruman fina-finan Hausa na Kannywood na wanni kallo a matsayin mutanen da basa son yin aure musamman ma matansu da wasu ke ganin rayuwar da suke ba ta dace da addini da al’ada ba.
To sai dai dama an ce ba duka ne aka taru aka zama daya ba, domin kuwa duk inda mutane da yawa suka taru to a cikinsu za’a samu masu tunani wanda ya sha banban dana sauran, duba da irin yadda wasu daga cikin jaruman tuni suka yi aurensu kuma suke zaune a gidan mazajensu.
Fitacciyar jarumar a Kannywood kuma jigo a siyasar jihar Kano, Rashida Adamu Abdullahi wacce aka fi sani da Rashida Mai Sa’a, ta bayyana babban abinda ke gabanta yanzu.
Jarumar ta bayyana haka ne jiya a shafinta na Instagram inda ta bayyana aure a matsayin abinda take babban buri a rayuwarta na yanzu.
Ta ce matukar ta samu mijin aure mai sonta tsakani da Allah babu makawa za ta aure shi.
Ta ce: “Aure shine babbar damuwata a yanzu. Allah kabani miji nagari abokin arzikina”.
Idan ba a manta ba a baya jarumar ta taba yin wata magana, inda ta bayyana cewa samun mazan aure na yi musu wuya, musamman ma su jaruman Kannywood.
Me Zakuci ‘yan Uwa Ku Ajiye Munah Ra’ayoyin Ku A Nan Kasa.