Jarumi Sahir Abdoul Yasha Zagi da Tsinuwa Akan Wata Faifan Bidiyo dayayi

0

Tirƙashi Jarumi Sahir Abdoul Yasha Zagi da Tsinuwa Akan Wata Faifan Bidiyo daya Dora Dauke da Zane da Yayiwa Hannun sa.

Fitaccen Jarumi a Masana’antar Kannywood Sahir Abdul wanda akafi sani da Malam Ali Acikin Shiri me dogon Zango Kwana Casa’in yasha zagi da Tsinuwa hade da bakaken Maganganu bayan wata faifan bidiyo daya wallafa.

Jarumin ya wallafa wata faifan bidiyo ne a shafinsa na Tiktok Yayinda ake daukar sa a wurin motsa jiki a hannun sa kuma yayi wani zane wanda yayi kama da tattoo irin wanda Fitattun Mawaka da Yan Gwallo na kasashen turai sukeyi.

Har ila yau Kuma ya sake wallafa wasu Hotunan a shafinsa na Facebook dauke da wannan Zane a barin hannunsa na hagu inda ya bayyana cewa Jama’armu na Facebook Muna Gaisuwa Kuma Muna nan Muna Kara Sanku.

Bayyanar wannan Hotuna dai sune Suka Jawo cece Kuce a Tsakanin Dimbin Mabiyansa inda Sukaita Maida Martani wasu ma Harda zagi hade da bakaken Maganganu.

Sulaiman Shadda ya rubuta cewa Dan Allah ka daina zana tattoo a hannun ka domin wannan dabi’ar Kazaman turawa ne sannnan Allah Zai tamabayeka akansa.

Related Posts
1 of 405

Mannir A dogo shi kuma cewa yayi Assalamualaikum Shawarata a gareka wannan tatoo bai kamata agunka kaba kana dan musulmi ga iyali ga yaya bai wai ta haka zaka samu Soyayyar mutane ba wallahi sai dai su ragu idan kunne yaji

Irfan baye shima yayi nasa martanin cewa Ina Shari’a anan menene amfanin wannan Zanen a hannun ka? Mutuwa yanzu, injima, gobe idan tazo ta dauke ka me zaka fada?

Shin kasan ma’anar mutum yayin irin wannan zanen a jikinsa kuwa? gaskiya ka gyara.

Mannir Khalid kuwa cewa yayi wannan ba tattoo bane lalle ne wanda mata ke zanawa a jiki, ko uwar meyasa aketa tsanar sa? Kuma Zuciyar masu tsanar shi idan an duba ba mai kyau bace.

Karshe dai Zamu iya cewa yawancin Jarumai masu irin wannan abubuwan suna yine kawai don neman suna bawai don rashin sani ba.

to masu sauraron mu kada ku manta dai ku danna mana subscribe da kuma alamar kararawa domin samun sabbin shirye shiryen mu idan mun dora.

Kada kumanta kudanna mana Alamar kararrawar sanarwa domin samun jin kararrawar sanarwar shirye-shiryenmu Masu ƙayatar wa mungode.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More

Privacy & Cookies Policy