Jarumin Kannywood Adamsy Celebrity zai angwance da Ummakatty ran Asabar
Adams Celebrity da amarya Ummakatty
MATASHIN jarumi a Kannywood, Adam A. Adam, wanda aka fi sani da Adamsy Celebrity, zai angwance a ranar Asabar mai zuwa.
Za a ɗaura auren sa da sahibar sa Ummu-Khursum Muhammad Tamula (Ummakatty) a ranar Asabar, 10 ga Disamba, 2022, da misalin ƙarfe 11:00 na safe a masallacin Zawiyya, Zololo, Jos, Jihar Filato.
Adam A. Adam da Ummu-Khursum Muhammad Tamula
Mujallar Fim ta ruwaito cewa Adamsy Celebrity jarumi ne, amma an fi sanin sa a ɓangaren bidiyon waƙoƙi, kamar yadda sauran matasan jarumai ke yi yanzu.
Allah ya sa a yi a sa’a, amin.
Ango Adam da amarya Ummu-Khursum