Jarumin Kannywood Yusuf Saseen zai zama angon Amina ranar Asabar mai zuwa
Yusuf Saseen (a dama shi ne a wajen wasan ƙwallon ƙafar bikin sa da aka buga)
JARUMI a Kannywood, Yusuf M. Abdullahi (Saseen) zai angwance a ranar Asabar mai zuwa, 24 ga Disamba, 2022.
Jarumin na ci gaba da raba katin gayyatar bikin auren a soshiyal midiya.
Kamar yadda katin ya nuna, za a ɗaura auren Saseen da masoyiyar, Amina Zakari Yunusa Daya, a gidan Makaman Fika, da ke layin makaranta a garin Potiskum cikin Jihar Yobe.
Ango a tsakiyar ƙungiyoyin ƙwallon ƙafar bikin sa a filin wasan
Bugu da ƙari, a daren ranar Lahadi aka buɗe shagalin bikin da wasan ƙwallon ƙafa da aka buga tsakanin ƙungiyoyi biyu, ‘Team Kannywood’ da Saseen Friends Team’. An buga wasan a filin wasa na Ɗan Nagari da ke Sultan Road a Kano.
Bayan ɗaurin aure ran Asabar, a ranar Lahadi kuma za a yi walima.
Sai dai kuma har zuwa yanzu ba a ga hotunan kafin aure (pre-wedding pictures) ba, kar yadda sauran jarumai ke yi.
Mujallar Fim ta ruwaito cewa Saseen shi ne Lukman, saurayin Sumayya a cikin shirin ‘Labari Na’, mai dogon zango na darakta Malam Aminu Saira.