Magana ta ƙare: Jarumar Kannywood Khadija Yobe za ta auri tsohon saurayin ta

0

Magana ta ƙare: Jarumar Kannywood Khadija Yobe za ta auri tsohon saurayin ta - Kannywood - News, reviews and more › hausa

Khadija Sani Yobe

A YANZU haka shirye-shirye sun yin nisa na bikin jarumar Kannywood Khadija Sani Yobe, wadda aka fi sani da Karima a cikin shirin ‘Izzar So’.

Za a yi bikin ta a cikin watan Fabarairu, 2023, idan Allah ya kai mu.

Wata majiya ta faɗa wa mujallar Fim cewa jarumar za ta auri wani tsohon saurayin ta ne wanda su ka daɗe su na soyayya, tun kafin ta shiga harkar fim.

Related Posts
1 of 405

Duk da yake wakilin mu ya yi ƙoƙarin yin magana da Khadija, bai same ta ba, amma dai ɗaya daga cikin matan da su ka fi kusanci da ita a cikin harkar fim, wato Asma’u Sani, ta tabbatar mana da gaskiyar maganar auren.

Khadija Yobe (Karima ta cikin ‘Izzar So’)

Hajiya Asma’u ta ce har ma an fitar da kalar ankon da za a yi a bikin, kuma ta ce da saurayin na Khadija sunan sa Izuddin wanda shi na ɗan Jihar Yobe ne.

Ta ƙara da cewa Izuddin mawaƙi ne sannan mataimaki na musamman ne ga gwamnan Yobe.

Cikin shirin bikin, nan da ɗan wani lokaci Khadija za ta tafi Saudiyya domin yin Umrah, bayan ta dawo sai a ci gaba da shirin bikin.

Daga cikin jerin shagulgulan bikin an shirya za a yi babban taron biki na ‘yan fim zalla a Kano, daga nan sai rankaya a tafi Jihar Yobe domin ci gaba da bukukuwan har zuwa ɗaurin aure da kuma tarewar amarya.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More

Privacy & Cookies Policy