Mansur Makeup da Amina sun samu Afreen
Maimunatu (Afreen) da iyayen ta, Mansur da Amina
A RANAR Asabar, 10 ga Disamba, 2022 Allah ya azurta mai kwalliya a Kannywood, Mansur Isma’il, wanda aka fi sani da Mansur Makeup, da ‘ya mace.
Matar sa Amina Murtala Kwacciɗo (Mummy) ta haifi santaleliyar ‘yar da misalin ƙarfe 7:30 na safe, a wani asibitin kuɗi mai suna Faris Hospital and Maternity da ke Titin Swimming Pool, Shooting Range, Kabala, Kaduna.
An raɗa wa jaririya suna Maimunatu, amma su na kiran ta da Afreen.
Mujallar Fim ta ruwaito cewa za a yi shagalin bikin suna a ranar mai zuwa Asabar, 17 ga Disamba, a gidan Mansur da ke Lamba K3, Abaji Road, Shooting Range, Kabalan Doki, Kaduna.
Mujallar Fim ta ba da labarin ɗaurin auren Mansur da Mummy da aka yi a ranar Asabar, 8 ga Janairu, 2022, a masallacin Rahamaniyya da ke Sabon Fegi, Gusau, Jihar Zamfara. Ga shi har Allah ya albarkace su da haihuwa.
Allah ya raya Afreen bisa tafarkin Manzon Allah (s.a.w.), amin.