Mansura Isah Itace Kan Gaba Wajen Kawo Zaman Lafiya A Masana’antar Kannywood

0
IMG 20200201 083034 108

Tsohuwar jarumar Kannywood, Mansura Isa ta wadda ta kasance guda daga cikin jarumai mata wadanda suka taka muhimmiyar rawa a Kannywood tun duniya ta na kwance. Jaruma ce da ta yi tashe a wancan lokacin domin idan a na kiran sunayen jarumai mata za a sakata a jerin farko na manyan jarumai mata na lokacin.

Sai dai kuma tun bayan auren ta da Jarumi Sani Danja a ka dai na jin duriyar ta sai daga baya bayan nan.

Mansura Isa ta koma gefe guda inda ta bude cibiyar tallafawa marayu  mai suna Todays Life Foundation, wadda ta yi kaurin suna wajen tallafawa marayu marasa lafiya da dai sauransu. Har ila yau jarumar ta na daya daga cikin matan dake tofa albarkacin bakin su a duk lokacin da wata matsala ta taso domin samun gyara a cikin al’umma baki daya.

Misali akwai lokacin da a ka samu sabani tsakanin Sadiya Haruna da saurayin ta Isa A Isa, wadda ta shiga cikin maganar tare da yin sulhu, duk da hakan ba ta yiwu yadda yakamata ba, amma ta zaunar da Sadiya ta nu na mata illar yin hakan.

Mansura ta ce “Wani abun muna hakuri mubar, ba don kan mu ba sai don mutuncin da ‘ya’yan mu, Sadiya, idan muka ce komai a kayi mana zamu dauki mataki a kai daga baya sai muzo muna danasani, misali ni yanzu fim na yi a baya amma wannan abun kadai ya shafi ‘ya’ya na musamman a makaranta bare irin wannan abun da ki ke yi.”

Related Posts
1 of 405

Bayan nan kuma an samu wani ce-ce-kuce a shafin sada zumunta na instagram bayan dora tsohon hoton jaruma Rahma Sadau da wani fitaccen shafi ya wallafa a lokacin an samu ce-ce-kuce sosai domin mutane sun yi ta yada maganar sakamakon hoton da ya kasance jarumar ta na sanye da hijab wannan dalili ya sa mutane suka rinka caccakarta har wata ta kai ga cewa jarumar ta ji kunya kuma Allah ya yi musu tsari tare da haifar mai irin dabi’ar ta.

A wannan lokacin tsohuwar jaruma Mansura Isa ta yi magana inda ta ja kunnen matar da yakamata ta rinka sanin abunvda zavta fada avkan ‘ya’yan wasu domin itama uwace abun da ka fada a kan dan wani idan mai kyau ne shi ya ke tasiri a kan naka, hakan nan idan kishiyar hakan ne. Kuma da wannan nasiha na Mansura Isa matar ta fahimci abun da ake nufi.

Har ila yau, batun Maryam Sanda wadda a ka yanke ma ta hukuncin kisa ta hanyar rataya sakamakon kashe mijinta da ta yi, Mansura Isa ta yi dogon sharhi a kan hakan tare da jawo hankalin mata kan su rinka rage kishi sannan su rinka kai zuciyar su nesa a kan rayuwa.

Tsohuwar jarumar ta ce” Babu inda a kace idan mace batayi aure ba, baza ta shiga aljanna ba idan har mace ba za ta iya hakuri da halin mijinta ba gudun samun matsala irin wannan sai ta hakura da auren babu dole”. Inji Mansura.

Ire-iren wadan nan shawarwari na Mansura Isa, kullum ta na tsayawa tsayin daka wajen ganin ta fahimtar da mata duba da irin yadda rikice-rikice ke yin yawa a yanzu.

Wannan dalili ya sanya majiyar mu ta Northflix yunkurin tattaunawa da tsohuwar jarumar, dangane da wannan al’amari sai dai hakan bai yu ba sakamakon kasa samun ta da muka yi ta wayar tarho watakila ko sai a nan gaba maji hanzarin ta na samar da masalaha da take yi a cikin masana’antar Kannywood.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More

Privacy & Cookies Policy