Martanin Datti Assalafy Kan Sabbin Hotunan Rahama Sadau.

0

Martanin Datti Assalafy Kan Sabbin Hotunan Rahama Sadau.

Zazzafan Martanin Datti Assalafy Kan Wadannan Sabbin Hotunan Fitsara Da Jaruma Rahama Sadau Ta Saki. Dan Jaridar Yayi Rubutu Sosai Game Da Jarumar, Dama Kuma Tun Kafin Yanzun Assalafin Yana Takun SaQa Da Jaruman KannyWood Din.

Yayi Rubutu Akan Wannan Hotunan. Inda Yayi Rubutun A Shafinsa Na Facebook. Ga Abin Da Yake Cewa.

Rahama Sadau

MASU KOYAR DA TARBIYYA

Shahararriyar jaruma a masana’antar Hausa film Rahama Sadau ta saki wasu zafafa hotuna na fitsara da gashin doki a kanta domin matan Musulmi suyi koyi da ita

Related Posts
1 of 405

Jama’a wadannan sune karnukan farautar Yahudu da nasara wadanda ake cewa suna koya mana tarbiyya da fadakarwa a Kasar Hausa

To kunga irin tarbiyyan da kuma fadakarwan, ko wacce bata da addini ne tayi irin wannan shiga za’a iya cewa ta fitsare, balle Musulma da aka haifeta cikin Musulunci

Na tabbata kafin Rahama Sadau ta shiga Hausafilm ko nawa za’a bata ba zatayi irin wannan shigar ba, amma kunga abinda shiga masana’antar Hausa film ya kai ta ya baro tana ‘yar Musulma

Kuyi hakuri da ganin hotunan, muna sakawa ne domin ya zama hujja kar a zargemu cewa sharri muke musu, kuma mun damu da su ne saboda ance masu koya mana tarbiyya ne, amma abinda muke gani masu lalata mana tarbiyya ne

Duk Musulmin da ya wayi gari ya ga ‘yar sa tayi irin wannan shigar abinda zai fada a ransa shine ko tayi ridda ne?, don ko ‘yar [email protected] ce Musulma tayi irin wannan shiga sai ta bada mamaki

Allah Ka shiryar da ‘yan Hausa film, Ka kare Musulmai daga sharrinsu اللَّهم آمين

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More

Privacy & Cookies Policy