Masana’antar Kannywood Ta Kaddamar Da Sabuwar Doka Mai Dauke Da Sabbin Riguna

AJIYA LITININ 27 GA WATAN JANUARY 2020.
Shugaban hukumar tace fina finai na jihar Kano Malam Ismael Naabba Afakallah ya kaddamar da riguna na musammam wadanda maaikatan hukumar zasu dinga amfani dasu a duk lokacin da zasu fita Operation, an gudanar ds taron raba rigunan a ofishin babban Director dake Headquarter din maaikatar, an bawa shugabannin Department na hukumar tare da direktoci, sannan aka bawa maaikatan dake fita aikin Operation.

Bayan kammala bukin raba rigunan, sai nan take maaikatan hukumar kamar yadda suka saba, suka fita aiki inda suka ziyarci wajen shakatawa na Munjibir Pack dake Munjibir local Government, suka duba masu shirya film da sune aikin daukar sabon film a wajen, maaikatan sun tantance domin ganin ko akwai wadanda basuyi rigista da hukumar ba.

A karshe shugaban hukumar Malam Afakallah yayi kira ga maaikatan hukumar da su kara tsage dantse wajen gudanar da ayyukansu ta yadda kowanne a cikinsu zai zama Afakallah a nasa ofishin.



