Masu Kutse Sun Kwacewa Sadiya Gyale Abinda Ta Mallaka A Shafin Internet Mafi Soyuwa A Gareta

A shafin na fitacciyar jarumar, wato @real_gyale_ sun tura wani saƙo wanda ke kira ga masu bin shafin nata da su saka kuɗi a asusun wani wai shi Mr_Usman_Kabiru01, wanda ya kira kan shi da “Investment Blog”.
Da mu ka bincika sai mu ka gano cewa sunan ƙarya ne.
Shafin ƙarya na masu damfarar ya na da mabiya 1,650, ya na ɗauke da saƙwanni 307 yayin da kuma ya ke bin shafuka 5,216 a Instagram.
Mujallar ta gano cewa su na da shafuka irin wannan masu ɗimbin yawa, kuma yawanci su na ɗauke ne da sunan ‘Mr Usman Kabiru’.
Kalli Video Yadda Zaiyanu Dan Wasan Tauri Na Zamfara ke Wasa:-
Shafin ‘yan damfarar ya nuna cewar ya na da gidan yana mai suna www.binomo.com.
An fara tura saƙo a shafin nasu a ranar 11 ga Yuli, 2019. Daga nan aka ci gaba ana tura saƙwannin da ke shafa wa mutane mai a baki game da yadda za su samu babbar riba idan su ka zuba jari a kamfanin.
An yi watanni kafin ranar 12 ga Janairu, 2020 sannan su ka liƙa hoton wani matashi mai saje wanda su ke so su nuna kamar shi ne mai kamfanin.
Ashe shi wannan matashi sunan sa Ibrahim Rabo, kuma ma’aikacin Gwamnatin Tarayya ne. Da wata ta ja hankalin sa ga labarin da Fim ta wallafa a Instagram, sai ya kada baki ya ce, “Shegu ‘yan 419 team. Allah ya shirye su.”

Sadiya ta tabbatar wa da mujallar Fim cewa, “An yi ‘hacking account’ ɗi na ne.”
Ta yi kira ga masoyan ta da duk masu bin shafin nata da su kiyaye da cewa ba ita ce ta tura saƙon ƙarshe da ke kan shafin a yanzu ba, kuma ba ta damar tura saƙo a shafin, saboda haka kada su bari wani ya zambace su.
Ƙarin Bayani: Jim kaɗan bayan mujallar Fim ta fallasa su a Instagram, sai ‘yan 419 ɗin su ka yi bulokin ɗin mujallar daga shafin Sadiya Gyale da su ka yi hakin, da sauran shafukan da su ke damfarar mutane da su.
To Ayi hattara dai!, Ku Kasance Tare Damu A Shafin www.PressHausa.Com A Koda Yaushe Domin Samun Sabbin Labaran Kannywood.