Mawaƙi SS Danko zai zama ‘mai igiya biyu’ Juma’a mai zuwa
Ibrahim SS Danko da Nusaiba Shu’aibu za su zama ɗaya nan da kwana biyu
MAWAƘIN siyasa a Kannywood, Ibrahim Shehu Suleiman, wanda aka fi sani da SS Danko, shi ma ya yunƙoro zai ƙara aure kafin shekarar nan ta ƙare, domin kuwa yau saura kwana biyu ya zama mai igiya biyu.
Za a ɗaura auren SS Danko da sahibar sa, Nusaiba Shu’aibu, a ranar Juma’a, 23 ga Disamba, 2022.
Ibrahim SS Danko
Katin ɗaurin auren, wanda mujallar Fim ta samu, ya nuna cewa za a ɗaura auren da misalin ƙarfe 2:30 na rana a Ƙofar Gayan, daura da Kogoro, Zone II, lamba 17, Abbas Street, Zariya, Jihar Kaduna.
Wakilin mu ya ruwaito cewa SS Danko ya yi auren sa na farko a Mayun shekarar 2018.
Haka kuma shi ne babban mawaƙin ɗan takarar zama sanatan Kano ta tsakiya, A.A. Zaura.
Katin ɗaurin auren Ibrahim da Nusaiba