Mutum shida Da suka mutu, 16 suka jikkata a hatsari mota

0

Innalillahi wasu Mutum shida Da suka mutu, 16 suka jikkata a hatsari mota a jihar Bauchi

Akalla mutum shida ne suka mutu a wani mummunan hatsarin mota da ya auku ranar Lahadi a daidai ƙauyen Miya da ke ƙaramar hukumar Ganjuwa a jihar Bauchi da ke arewa maso gabashin Najeriya.

Babban kwamandan hukumar kiyaye aukuwar hadura mai lura da shiyyar yankin Yusuf Abdullahi ne ya bayyana haka cikin wani rahoton aukuwar haɗura da ya aike wa kamfanin dillancin labaran ƙasar NAN ranar Lahadi a Bauchi.

Babban kwamandan na hukumar FRSC ya ce wasu ƙarin mutum 16 sun samu raunuka sakamakon hatsarin.

Related Posts
1 of 407


Lamarin ya rutsa da motar ɗaukar fasinja guda ɗaya ƙirar Toyota Hiace, da safiyar ranar Lahadi.

Ya kuma alaƙanta faruwar hatsarin da fashewar taya tare da kwacewar motar.

Ya ƙara da cewa “mutum shida sun rasa rayukansu manyan mata biyu da ƙananan yara huɗu”.

Yusuf Abdullahi ya ce an kai gawarwakin waɗanda suka mutu da sauran waɗanda suka jikkatan babban asibitin Kafin Madaki .

Kada kumanta kudanna mana Alamar kararrawar sanarwa domin samun jin kararrawar sanarwar shirye-shiryenmu Masu ƙayatar wa mungode.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More

Privacy & Cookies Policy