Na Kusa Daina Waka, Na Koma Makarancin Al’Qur’ani
Na Kusan Daina Waka Kwata Kwata Nan Bada Jimawa Ba, Zan Koma Makarancin Al’Qur’ani Maigirma, – Mawaki Ali Jita, Mawakin Ya Bayyana Hakan Ne A Wata Sanarwa Daya Fitar A Shafin Tiwita,
Hakan Yasa Mutane Su Cika Da Mamaki, Inda Kowa Ke Tofa AlbarKacin Bakinsa Kan Wannan Kalami Na Shahararren Mawakin, Ali Jita Dai Mawaki Ne Da Duniya Ta Dade Tana Yayinsa, Inda Mawakin Ya Shafe Sama Da Shekaru Goma Sha Biyar Yana Sakin Wakoki Ba Tare Daya Sami Koma Baya A Bangaren Nashi Ba.
Masu Sharhi Suna Ganin Wata Shiriya Ce Tazo Mishi, Domin Kuwa Ba Karamin Nasara Bace Ace Mutumin Daya Shafe Irin Wannnan Shekaru Yana Sakin Wakoki, Rana Guda Aji Ya Aje Wakar Ya Koma Karatun Al’Qur’ani Mai Girma.
Mai Sharhin Nan Datti Assalafy Yayi Sharhi Dangane Da Wannan Lamarin Na Maganar Ali Jita. Inda Yayi Rubutu Kamar Haka
SHIRIYA DAGA ALLAH
Shahararren mawaki Ali Jita ya wallafa sanarwa a shafinsa na Twitter yace kwanan nan zai ajiye sana’ar waka, zai koma ga neman ilmin Qur’ani yana son ya zama daya daga cikin shahararrun makaranta Qur’ani na duniya da ba’a taba samu ba
Hakika wannan shiriya ne daga Allah ta zo wa Ali Jita, domin sana’ar waka da kida a Musulunci haramun ne, zai canza sana’a zai koma ga Qur’ani
Abinda ya rage wa Ali Jita shine ya nemi ilmin Qur’anin saboda Allah ba wai don neman shahara a gurin mutane ba, idan yayi don Allah zai samu lada a gurin Allah, idan yayi don neman shahara ba lada
Muna rokon Allah Madaukakin Sarki Ya cika masa burinsa da namu