Ni Mutuniyar Kirki CE, Inji Jaruma Hadiza Gabon

wani shiri da BBC Hausa ke kawo wa na hira da fitattun jarumai kan wasu abubuwa da suka shafi rayuwarsu.
A wannan karon, shirin na ‘Daga bakin mai ita ya tattauna da jaruma Hadiza Gabon’ fitacciyar tauraruwa ta fina-finan Hausa.
A cikin hirar jarumar ta bayyana abubuwa da dama da suka shafi rayuwarta, ciki kuwa harda inda take hango kanta nan da shekara biyar, da kuma wasu muhimman abubuwa.
Da aka tambayeta fatan da take yiwa kanta nan da shekara biyar, jarumar ta ce: “Aure, haihuwa, arziki Insha Allah .”
Haka da aka yi mata magana akan kwalliya jarumar ta ce ita ba ta cika yin kwalliya ba ko yanzu da tayi kwalliya ta yi ne saboda za ta zo hira da BBC din.
A bangaren tambayar ko tana da saurayi a Kannywood kuwa, jarumar ta tintsire da dariya ta ce: “Ka da ka kashe mini kasuwa mana, duk ‘yan uwana ne a Kannywood.
Wata tambaya da aka yi mata akan ta bayyana abubuwa guda uku game da ita, jarumar ta ce: “Ni mutuniyar kirki ce tabbas, kuma tara ce ba ta cika goma ba, dan adam dama ajizi ne, muna kuskure muna laifi .” A karshe jarumar ta kasa bayyana na ukun inda ta bukaci a ba ta dama ta kara maimaita cewa ita mutuniyar kirki ce.
Wannan dai kadan daga cikin tambayoyin da aka yiwa jarumar kenan.
Jarumar dai ita ce wacce aka yi ta faman tataburza da ita a shekarar da ta gabata tsakaninta da jaruma Amina Amal, inda take yi mata zargin madigo, lamarin da ya kai ga har sai da aka shiga kotu.
Jaruman dai har yanzu suna nan akan maganarsu ta cewa suna gyaran tarbiyya ne.