Nunu, ‘yar jaruman Kannywood Samira Ahmad da TY Shaban, ta cika shekara 9
Aisha TY Shaban (Nunu)
ITA ma tsohuwar jarumar Kannywood Samira Ahmad girma ya fara kama ta har ta fara shiga sahun manya, ko da kuwa ba ta yarda shekarun ta sun kai ba, to kuwa dole ta bar wa ‘yar ta yarintar, domin kuwa a yanzu dai ‘yar ta Aisha, wadda ake kira Nunu, ta cika shekara tara da haihuwa.
A ranar Juma’a, 16 ga Disamba, 2022 aka yi taron bikin zagayowar ranar haihuwar Nunu, wadda Samira ta haifa tare da .da suka haifa da jarumi, furodusa kuma mawaƙi T.Y. Shaban.
Nunu tare da mahaifiyar ta, Samira Ahmad
Hajiya Samira ta shirya wani taro na musamman a Kano domin taya ‘yar tasu murnar zagayowar ranar haihuwar ta, inda ta gayyato ƙawayen ta da kuma yara ƙawayen Nunu ɗin aka sha nishaɗi tare da abinci da abin sha, daga ƙarshe kuma aka yanka kek.
An yi taron an gama lafiya. Allah ya ƙaro shekaru masu albarka.
Nunu tare da mahaifiyar ta da kakar ta
Ƙawayen Samira da su ka haɗa da Fauziyya Maikyau, Ruƙayya Dawayya da Zahra’u Shata a wajen bikin zagayowar ranar haihuwar Nunu
Aisha Nunu cike da farin ciki