Ra’ayoyin ma’aurata kan dacewa ko rashin dacewar hana mata amfani da kafofin sada zumunta

0

Wannan sune Ra'ayoyin ma'aurata kan dacewa ko rashin dacewar hana mata amfani da kafofin sada zumunta

Ma’aurata sun bayyana ra’ayoyin su akan shin ya dace miji ya bar matarsa ta cigaba da yin amfani da kafafen sada zumunta na zamani.

Sai dai ra’ayi ya bambanta inda wasu suka goyi bayan maza su hana matansu wasu kuwa suka soki hakan.

A cikin wannan bidiyon za ku ji yadda maza da matan aure suka bayyana ra’ayoyin su kan dacewa da yin amfani da kafafen sada zumunta na zamani

Yadda barin jikin Magidanci ya shanye ɓayan matarsa ta sanar da shi cewa ba shi bane asalin mahaifin yaransu 2

Wani dan Najeriya ya bayyana tashin hankalin da wani mutum ya shiga bayan matarsa ta sanar da shi cewa yaransu biyu ba nashi bane, ta ruwaito.

Kamar yadda @MeverickThamani ya bayyana a shafinsa ba Twitter, mutumin ya kai shekaru 50 da doriya kuma ‘yar uwarsa ce yanzu haka take kulawa da shi a asibiti sanna ita ce ta bayar da labarin abinda ya same shi.

Related Posts
1 of 405

Ta ce mutumin yana matukar kaunar matarsa wanda hakan yasa ya zabe ta a maimakon ‘yan uwansa. A bayan har yanke alaka yayi da ‘yan uwansa sai daga baya ya kama ta tana lalata da wani namiji .

Wannan ne ya janyo rikici ya barke tsakaninsu har ta kai ga sanar da shi cewa yaransu ba nashi bane. Ana tsaka da rikicin ne ta bayyana masa wannan mummunan labarin wanda yasa ya fadi kasa bayan ya yanke jiki, hakan yayi sanadiyyar shanyewar barin jikinsa.

Bayan ganin halin da yake ne matar ta tsere ta kwashe kudi daga asusun bankinsa tare da guduwa da yaran. Yanzu haka yana zama ne karkashin ‘yan uwansa inda suke kulawa da shi kamar yadda mutumin ya bayyana a Twitter.

Wani labari Ban san ina da ciki ba, inji budurwar da ta haihu a jirgin sama

 Matar mai suna Tamara ta kwashi hanya ne zata wuce Ecuador daga Madrid, Spain a jirgin KLM Royal Dutch.

An samu bayani kan yadda Tamara kwatsam ta hau jirgi wanda ana gab da isa Netherlands ta fara jin ciwon ciki. Sakamakon jin ciwo, Tamara ta nufi bandaki inda ta nemi yin bayan gida kawai sai haihuwa ta yi.

Kamar yadda Daily Star ta ruwaito, Tamara ta haihu ne bayan yunkurin nakuda biyu.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More

Privacy & Cookies Policy