Rashin Biyayyah Ne Yasa Masana’antar Kannywood Ke Tabarbarewa

RASHIN tarbiyya da ƙin girmama na gaba na daga cikin manyan matsalolin da ke addabar masana’antar finafinan Hausa ta Kannywood, a cewar wani dattijo a harkar, wato Malam Adamu Muhammad ‘Kwabon Masoyi’.
Ya bayyana hakan ne a lokacin da ya ke tattaunawa da mujallar Fim kan halin da masana’antar ta tsinci kan ta a yau.
A cewar sa, “Ita harkar fim a matsayin ta na masana’anta, ta samar da ɗimbin ayyukan yi ga matasa wanda kuma hakan wani cigaba ne da aka samu, amma babbar matsalar harkar a yanzu ita ce ƙarancin tarbiyyar yaran.
Kalli Yadda Anka Fasawa Yaro Kai Wajrn Wasan Tauri:-
“Sau da yawa za ka je waje sai ka ga ba a ma damu da zuwan ka ba, ba a san kai wani ne ba.
“Amma dai duk da haka, ni a matsayi na na Adamu Muhammad zan iya cewa ba ni da matsala da kowa sai dai wadda ta shafi harkar baki ɗaya.”
A game da yadda za a tunkari matsalar, tsohon babban furodusan ya ce, “Kiran da zan yi shi ne su sa hankali a cikin aikin su, su cire ƙyashi da hassada, su rinƙa taimakon junan su, domin hassada da ƙyashi ne ya ke kawo faɗace-faɗace da tozarta juna, ta yadda har aka samu kai a halin da ake ciki a yanzu.”
Malam Adamu ya ƙara da cewa, “Harkar fim sana’a ce, don haka su daina ɗaukar ta da wasa, kamar yadda su ke yi mata a yanzu, domin su na ɗaukar ta a matsayin wasa ko wani dandalin nishaɗi.
“Saboda haka a rinƙa kiyayewa da kuma girmama juna, domin duk harkar da za ka ci ka sha ka yi wa kan ka sutura, to bai kamata ka ɗauke ta da wasa ba.
“Don haka a rinƙa kiyaye mutuncin ita kan ta sana’ar domin guje wa abin da mutane za su rinƙa ganin an yi abin da bai dace ba.”
Shi dai Adamu Muhammad, tare da shi aka yanke wa masana’antar finafinan Hausa cibiya, domin kuwa ya na daga cikin furodusoshin farko.
Fim ɗin sa mai suna ‘Kwabon Masoyi’, wanda ake yi masa laƙabi da shi, ya na daga cikin finafinan da aka soma shiryawa aka fitar zuwa kasuwa.
Amma yawancin ‘yan fim na yanzu, musamman irin yara-yaran nan, ba su ma san da zaman dattawan harkar fim irin sa ba ballantana su ba su wata ƙima.
Karanta:- Da Karshe Masana’antar Kannywood Ta Farantawa Maryam Booth.