Shari’ar Abdul jabbar abun da ya kamata kusani akan kisan Abdul jabbar ɗin

0

Tofa! Shari’ar Abdul jabbar abun da ya kamata kusani akan kisan Abdul jabbar ɗin

Duk wanda ya shigo ya kama yatsaya ya karan ta wannan bayanin akan malam abdul jabbar nasir kabara wanda aka yan kewa hukincin kisa ta hanyar rataya birnin Kano a ranar al’hamis.

“Na yarda Mallam Abduljabbar ya yí Mãnyan laifúka gúda huɗu – Áliyu Ɗahíru Aliyú.

Ya yí fada da Salafíyya.
Ya yí fada da yan haqíqa.
Ya yi fada da wasú yan Qadiríyya
Ya yí fada da wasú yan síyasa.

Wadannan sú súka hadu súka mayar da fadansu céwa na zagín Annabí (saw) né alhalin su kansu sun san karya suke.

Nì daí da Annabi (saw) ya yí arahar da zan yì siyasa da shi, gwara a yau rayuwata ta fi. Anya wasu sun yarda idan an mutu za a tashi kuwa?

Na yi imani bayan wannan rayuwar akwai wata rayuwar mafi muhimmanci da adalci. Ta yaya zan iya kallo Annabi (saw) a ranar alkiyama tare da na san na yi amfani da shi a duniya wajen bukatuna?

Related Posts
1 of 405

Zan iya mutuwa a yanzu-yanzu ko an jima. Ko wani bai kasheni ba, zan mutu a gida ko asibiti. Daga karshe dai duk mutuwa zamu yi ko mun shirya ko bamu shirya ba, kuma babban abin da zamu tarar shi ne abin da muka kudirta ko muka aikata.

Fatana Ubangiji Ta’ala ya sa duk rintsi ya haneni siyasantar da addini ko karfafa masalahar duniyata fiye da ta lahirata. Ubangiji kada ka bari rashin tsoronka ya sa mu aikata zalinci da sunanka ko mu goyi bayan zaluncí da súnanka.

ماذا تقول؟

Mé za kúce ?

DA ƊUMI-ƊUMI: Kotu a Kano ta yanke wa Abduljabbar hukuncin kisa

Wata Kotun Shari’ar Musulunci da ke zamanta a Kofar Kudu a Jihar Kano, karkashin jagorancin Ibrahim Sarki Yola, a yau Alhamis ta yanke hukuncin kisa ta hanyar rataya ga malamin addinin Musulunci, Sheikh Abduljabbar Kabara.

Daily Nigerian Hausa ta ruwaito cewa an maka Kabara a kotu ne bisa wasu kalamai na batanci ga Annabi Muhammad (SAW) a wajen karaturruka sa.

Kada kumanta kudanna mana Alamar kararrawar sanarwa domin samun jin kararrawar sanarwar shirye-shiryenmu Masu ƙayatar wa mungode.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More

Privacy & Cookies Policy