Shekara 10 da aure: Ina alfahari da zama na da Sumayya, inji Jamilu Ibrahim
Sumayya da Jamilu Ibrahim
JARUMIN Kannywood, Jamilu Ibrahim (Home Alone), ya bayyana godiyar sa ga Allah da ya nuna masu cika shekara goma tare da da matar sa Sumayya cikin zaman lafiya da ƙaruwar arziki.
An ɗaura auren Jamilu da Sumayya, wadda ‘yar fitacciyar jaruma Asma’u Sani ce, a ranar 24 ga Nuwamba, 2012.
Allah ya albarkaci auren da ‘ya’ya huɗu – maza uku da ƙanwar su.
Jamilu da Sumayya tare da ‘ya’yan su
A tattaunawar sa da mujallar Fim Jamilu ya ce: “Alhamdu lillah, babu abin da za mu ce ni da mata ta Sumayya sai dai mu ƙara godiya ga Allah.
“Yau ga shi mun cika shekaru goma da auren mu kuma babu abin da ya ke cikin zaman auren sai zaman lafiya da fahimtar juna.
“Kuma ga shi Allah ya yi mana arzikin ‘ya’ya har guda huɗu. Don haka abin alfahari ne a gare mu tare da dukkan masoyan mu.
“Fatan mu shi ne Allah ya ƙara mana zaman lafiya da fahimtar juna da ƙaruwar arziki, kuma Allah ya raya mana yaran mu yadda za mu yi alfahari da su, su ma su yi alfahari da mu.”
Ita ma Hajiya Asma’u Sani da mu ka nemi jin ta bakin ta a game da cikar auren Jamilu da Sumayya shekara goma, farin ciki da hamdala ta yi.
Ta ce: “A gaskiya ina farin ciki sosai, domin a yadda yanayin rayuwa ya ke da kuma zaman aure a wannan lokacin, har aka cika shekaru goma ai dole na yi murna kuma na yi alfahari da wannan zaman aure.”
Ta ci gaba da cewa, “Kuma a gaskiya Jamilu Ibrahim ya cika suruki, don ba ni ba, duk wanda ya san ni da shi, to Jamilu ya na girmama shi. Kuma babban abin alfahari na shi ne tsawon shekaru goma da su ka yi Sumayya ko yaji ba ta taɓa yi ba. Ka ga kuwa ai ya cika miji nagari.
“Ina godiya ga Allah. Kuma Allah ya ƙara masu zaman lafiya da fahimtar juna.”
Jamiu da Sumayya cikin murna
Jamilu da Sumayya sun yi bikin zagayowar ranar ɗaurin auren su ta hanyar yin abinci da kwalliya da hotuna na musamman su da ‘ya’yan su.
Ɗimbin jama’a daga cikin Kannywood da wajen ta sun taya su murna sosai tare da addu’ar Allah ya ƙara ƙauna da cigaba a rayuwar su ta zaman aure.
Sumayya da Jamilu a gaban kek da abincin murna
Ma’auratan masoya: Sumayya da Jamilu