Shin Da Gaske Ne Ankama Wanda Yayiwa Jaruma Mome Gobe Fyde

0

Shin Da Gaske Ne Ankama Wanda Yayiwa Jaruma Mome Gobe Fyde

Shin Da Gaske Ne Ankama Wanda Yayiwa Jaruma Mome Gobe Fyde

FYAƊE A MAHANGAR MU DA MAHANGAR SU.

MAL.AMINU IBRAHIM DAURAWA:

Musulunci ya haramta zina da madigo da luwaɗi da bin dabba da amfani da hannu, da amfani sashin jiki wajan biyan buƙata, ko amfani da azzakarin roba, ko yarbebi ta jima’i, ya hana auran jinsi mace da mace namiji da namiji, ya hana auran dabba da mutum kamar namiji ya auri karya ko mace ta auri kare, ya hana ɗaukar amarya,. wato fyaɗe,

Ya haramta duk wata hanya ta biyan bukatar sha’awa idan ba aure ba.

FYAƊE.

Abinda ake kira Fyaɗe shine yin amfani da ƙarfi, ko wata barazana, wajan tilasta wani ko wata wajan yin lalata, kamar namiji ya yi wa mace Fyaɗe ko mace ta yiwa namiji Fyaɗe, ko namiji ya yiwa namiji Fyaɗe ko mace ta yiwa mace Fyaɗe, ana yi wa yara Fyaɗe ana yi wa manya Fyaɗe, ana yi wa maza ana yiwa mata, amma a wajan turawa Fyaɗe ya haɗa da auran ƙananan yara da duk wani Shekaru da doka ba ta amince ba ayi aure, ko zina ko luwaɗi ba tare da cikar wannan shekaru ba shima yana cikin Fyaɗe, amma idan shekaru sun cika, kuma anyi da yarda da amincewar ɓangaran guda biyu, to wannan zina ko luwaɗi ko auran jinsi a wajan su ba laifi bane, wannan shine banbanci tsakanin fyaɗe a wajan turawa da mu, su sun hallata zina da liwadi da madigo da auran jinsi da auran mutum da dabba, mu kuwa wannan duka haram ne,

Don haka Fyaɗe shine yin zina da ƙarfi ko yin luwaɗi da ƙarfi ko yin maɗiko da ƙarfi, (suna saka auran wuri a cikin fyaɗe amma mu a wajan mu ko da wata kasa ta musulmi ta yanke shekarun aure ba za a ɗauki wanda ya yi auren wuri a matsayin wanda ya yi fyaɗe ba) idan aka yi waɗannan bisa yardar dukkan ɓangaran da amincewar su, wannan ba a kiran sa Fyaɗe, a wajan su. duk da ƙananan yara ba a yin lalata da su ko sun amince saboda ba su mallaki hankalin su ba, kuma ba susan abu mai cutarwa ko mai amfani ba. don haka yin amfani da ƙananan yara da basu mallaki hankalin su ba, laifi ta ko wacce hanya.

Abubuwan da zaa duba akan matsalar fyaɗe shine. Wasu matakai guda goma

1, kafa wani kwamiti mai ƙarfi wanda zai shafi dukkan masana, domin yin nazari akan yadda Fyaɗe yake faruwa

2. Shirya faɗakarwa akan yadda iyaye zasu sa ido akan ƴaƴansu, da kuma yadda zasu tsaya wajan neman haƙƙin su.

Related Posts
1 of 408


3. Wayar da kan al’umma akan illar yin fyaɗe, a dukkan mahaɗa ta al’umma.

4. Tilastawa asibitoci karɓar ces ɗin fyaɗe cikin gaggawa a ko wanne lokaci, domin idan babu rahotan likita ana shan wahala a kotu wajan tabbatar da faruwar abin har a ƙarshe wanda ake tuhuma ya kuɓuta.

5. Sanar da yan sanda ko ta kwana gamai da fyaɗe, domin tattara sheda kafin ta lalace, domin sai kaji a katu ance wane irin kaya ne a jikin sa.

6. Samawa iyaye lauya mara kwaɗayi, domin idan wanda ya yi fyaɗen mai gata ne, kuma waɗanda aka yiwa ƴarsu marasa ƙarfi ne sai a juya abin a kotu.

7. Samar da alƙalai masu tsoran Allah waɗanda zasu dinga duba maganar Fyaɗe bisa adalci da gaskiya, akan wanda ake zargi da wanda aka yiwa.

8. Cirewa mutane al’adar rashin bin haƙƙi, da kuma tsoran abinda zai sami yarinya bayan ta girma idan ƙarama ce, ko surutun jama’a idan babbace, cewa ba su da laifi a shari’a.

9. Kada a koma gefe a bawa iyaye kuɗi su janye tuhuma, idan wasu suna amfani da ƴaƴan talakawa, idan anje kotu sunga alamar zaa yi nasara sai su bawa iyayan maƙudan kuɗi sai su janye, wannan ma yana faruwa

10. Idan an tabbatar da laifi akan mutum babu wata shubuha ayi gaggawar yi masa hukunci, ba tare da ɓata lokaci ba.

11. Kuma a Samar da hukunci na bai ɗaya wanda zai zama ya tsawatar, babu sani babu sabo.

12. A Samar da kwararrun lokitoci da za su dinga duba lafiya waɗanda aka yiwa fyaɗe, da yi musu aiki domin ceto raunin da aka yi musu kuma kyauta.

HUKUNCIN FYAƊE A MUSULUNCI.

Malamai sunyi bayani akan yadda za a hukunta, mazinaci wanda shine irin hukuncin da ake yiwa mai fyaɗe, mai aure a jefe shi, mara aure ayi masa bulala ɗari kuma ayi masa ɗaurin shekara, ita kuma sai a duba yadda ya lalata ta, sai a ɗaura masa biyan kuɗi wanda zai zama tara ga abinda ya yi mata, wasu malamai sun kira shi sadakin auran ta, wasu kuma sun kira shi tara. idan kuma ya yi amfani da makami, sai a fassara shi a wajen wasu malaman da hiraba wato fashi, sai a kashe shi yadda ake kashe yan fashi da makami. Kamar ɓarawo ne da ɗan fashi duk sata sakayi amma shi ɗan fashi ya yi amfani da makami, wannan shine ra’ayin wasu malamai, waɗanda suke ganin zaa yiwa mai fyaɗe hukunci biyu idan yayi amfani da makami kamar yadda ƴan fashi suke yi suje gidan mutum suyi sata sannan su afkawa iyalan sa.

ALLAH SHINE MAFI SANI.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More

Privacy & Cookies Policy