Sirrin kawowar mu shekara 9 da aure: Hira da Yerima Shettima da tsohuwar jarumar Kannywood Fati Ladan

0

Sirrin kawowar mu shekara 9 da aure: Hira da Yerima Shettima da tsohuwar jarumar Kannywood Fati Ladan - Kannywood - News, reviews and more › hausa

Alhaji Yerima Shettima da Hajiya Fati Ladan

HAƘURI da juna tare da taimakon Allah su ne sirrin kaiwa shekara da aure da su ka yi, a cewar tsohuwar jarumar Kannywood Hajiya Fati Ladan da mijin ta, Alhaji Yerima Shettima.

Dangane da wannan abu, Fati ta bayyana godiyar ta ga Allah (s.w.t.) da ya ba su ikon kaiwa tsawon wannan lokaci.

Tsohuwar jarumar ta faɗi ne a yayin tattaunarwar ta da mujallar Fim a yau, lokacin da su ka gudanar da wata ƙwarya-ƙwaryar walimar murna cika shekara tara da aure a gidan su da ke Yerima Close, kan Titin Jinya, Kanta Road, Kaduna.

Fati ta ce, “Ina godiya ga Allah (s.w.t.) da ya nuna min wannan babbar rana da mu ka cika shekara tara da aure da miji na. A yau farin ciki na ba zai misaltu ba. Allah ya ƙara mana so da ƙaunar juna.”

Haka kuma ta yi godiya ga ‘yan’uwa da abokan arziƙi da su ka yi tattaki, su ka je taya ta wannan farin ciki, ta ce masu, “Na gode masu. Allah ya saka da alkhairi. Yadda kowa ya zo gidan nan lafiya, Allah ya mai da kowa gidan sa lafiya.”

“Duk inda jinjina ta ke, ya kamata a jinjina masa,” cewa Fati game da ƙoƙarin Yerima

Da mu ka tambaye ta abin da za ta ce wa maigidan ta, sai ta amsa da cewa, “Abin da zan ce wa maigida na shi ne ina godiya sosai da haƙuri da ni da kuma so da ƙauna da ya ke nuna min. Tun daga lokacin da mu ka yi aure har zuwa yau bai taɓa nuna min wani bambanci ko wani ƙyama ko wani abu haka dai. Gaskiya ina godiya sosai, don duk inda jinjina ta ke ya kamata a jinjina masa, saboda ya yi namijin ƙoƙari, don ya ba da gudunmawar shi sosai na ganin cewa mun kawo wannan mataki da mu ke kai yanzu. Domin haka ina yi masa godiya. Ubangiji ya saka masa da alkhairi, Allah ya tsare shi, ya ƙara haɗa kan mu gaba ɗaya iyalan shi, shi kuma Ubangiji ya ba shi sa’a a duk inda ya sa gaba.”

Yawanci sha’anin da Fati ke yi, a kan ga abokan sana’ar ta na da, amma a wannan karon babu ko mutum ɗaya daga cikin su. Mun tambaye ta dalilin hakan, sai ta amsa da cewa: “To gaskiya wannan karon ban gayyace su ba, ban kira su ba. Dalili, na ga ba zan yi taron biki ba ne sosai; na ɗan shirya ƙwarya-ƙwaryar walima ne tsakani na da maƙwabta na da makusanta na saboda na ga duk lokacin da taro ya tashi su kan zo su ba da gudunmawar su, kuma zai zama kamar wahala a gare su, shi ya sa na ce kowa ya huta yanzu. Wannan da mu ka yi, mun yi mu da ‘yan tsirarun abokai ne da ‘yan’uwa da abokan arziƙi da su ke kusa da ni.

“Duk wani da ke nesa ban kira shi na gayyace shi ba. Ba wai kuma don wani abu ba, sai dai kawai don ina buƙatar kowa ya zauna ya huta, su na yi min, kuma sun yi min, na gode. Kuma in Allah ya yarda ai ba a rabu ba, akwai gaba.”

A nasa ɓangaren, mijin ta, Alhaji Yerima Shettima, wanda shi ne shugaban Ƙungiyar Tuntuɓa ta Matasan Arewa (Arewa Youth Consultative Forum), ya ce, “Alhamdu lillahi. Godiya ta tabbata ga Allah maɗaukakin Sarki. Wannan ba ƙaramin abu ba ne da za ka iya kwatantawa ba, sai dai ka yi godiya ga Allah, saboda shekara tara ba wasa ba ne a rayuwa, bare rayuwar aure na zamani irin na yanzu da ya ke zuwa da jarabta iri-iri da kuma abubuwa.

Related Posts
1 of 408


“Ba iyawar mu ba ne, Allah ne ya ga dama, kuma Allah ne ya kare mu, har mu ka kai inda mu ka kai. Duk shekara idan ta juyo, mu na gode wa Allah, mu na kuma masu godiya.

“Kuma mu na kira ga ma’aurata: shi aure haƙuri ne, dukkan mu ‘ya’yan tara ne ba goma ba ne, ba za a ce an zauna ba za a saɓa wa juna ba, amma sai a yi haƙuri, in za a iya kaiwa shekara ɗari idan Allah ya ba da wannan damar, ka iya zaman auren ka ba tare da an samu wata matsala ba. Saboda haka ina kira, kowa ya zama mai haƙuri da amana. Tsakanin mata da miji sai Allah, a yi ta haƙuri da juna, babu gidan da ya ke ana zaune a ce ba a samun matsaloli, amma haƙuri ke sa a zauna tare, kuma a ci gaba da faɗa wa juna gaskiya. A sa Allah kuma a gaba. Wannan shi ne.”

Ko ya Yerima zai kwatanta tsawon shekarun nan da su ka yi da Fati? Amsa: “Wallahi sai hamdala, saboda na ji daɗin zama da ita, kuma ina kan jin daɗin zama da ita, domin kullum a ido na ganin abin na ke kamar sabo ne, kamar yanzu na kawo ta gida, kuma kamar na buɗe sabuwar mota ne, haka na ke kallon ta a ido na, saboda ana zama na mutunci, na ibada da kuma girmamawa daidai gwargwado.

“Na gode wa Allah, ga iyalai na gaba ɗaya. Da ita da wacce ta samu a matsayin uwargidan ta, dukkan su ina jin daɗin zama da su, mu na zaman lafiya, kuma babu matsala a tsakani na da su. Kuma har da ‘ya’ya na. Na gode Allah da ya ba ni wannan ƙarfin da kuma kwanciyar hankali.

“Don haka da waɗanda su ka zo taya mu murna da kuma waɗanda Allah bai ba su ikon zuwa ba, duk da cewa abin ba mu gayyaci mutane ba, mun yi shi ɗan daidai, amma duk da haka in ka na hulɗa da mutane, in ka yi kira sai ka ga sun halarta. Dukkan waɗanda su ka zo Allah ya mai da su gida lafiya. Mu na godiya.”

Mujallar Fim ta ruwaito cewa an fara walimar da misalin ƙarfe 5:30 na yamma, inda Yerima da abokan sa da ‘yan’uwan su su ka taru a wani ƙaramin falo da ke cikin gidan, ita kuma Fati ta yi tare da ƙawayen ta da kuma ‘yan’uwan ta a falon ta. An ci, an sha, har an gyatse.

Daga nan kuma sai aka haɗu gaba ɗaya a babban falon gida, inda aka yanka kek, sannan aka yi hotuna. Haka kuma mahalarta walimar sun yi wa ma’auratan addu’o’in samun cigaba da nasara a zaman auren su.

An tashi da misalin 6:30 na yamma.

“Kamar yanzu na kawo ta gida,” inji Yerima Shettima game da Fati Ladan

Wasu daga cikin waɗanda su ka halarci walimar sun haɗa da matan furodusa a Kannywood, Yakubu Lere, wato Hajiya Safiya da Hajiya Habiba, sai matar Adam A. Zango, Safiya Chalawa, Hassana ‘Yar’uwa da Hussaina.

An dai ɗaura auren Fati Ladan da Yerima Shettima a ranar Juma’a, 20 ga Disamba, 2013 a ƙofar gidan su Fatin da ke Unguwar Sarki, Kaduna.

A halin yanzu ‘ya’yan su biyu, Humaira da Amir.

Yerima Shettima da Fati Ladan sun ɗauki hotuna na musamman domin murnar wannan zango da su ka kai da aure
Fati da Yerima

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More

Privacy & Cookies Policy