Tirƙashi Bidiyan wata mata da ta tayar da kura a banki bayan an wawure mata kudi asusunta Innalilahi
Tambaya nan shin dasanin ban kuna ake haka ko babu sanin su?
Wata mata ta tayar da jijiyar wuya a banki bayan an wawushe mata maƙudan kuɗaɗe a asusun ajiyarta na banki, matar ta tayar da hargitsi a cikin harabar bankin, bayan ta gano cewa kuɗaɗenta dake a cikin asusun ajiyarta sun yi ɓatan dabo. Shafin Linda Ikeji ya rahoto.
Matar ta bayyana cewa ta sha yin ajiyar maƙudan kuɗaɗe a gidanta amma ko sau ɗaya ƴan fashi ba su taɓa yi mata sata ba, amma daga kawo kuɗi a banki kawai sai aka tattara ƴan kuɗaɗen nata da ta daɗe tana tarawa akayi awon gaba da su.
A cikin bidiyon wanda majiyar mu ta sanya a manhajar Instagram, an nuna matar nata kai kawo a cikin harabar bankin tana ta sharɓar kuka saboda kuɗinta da aka wawushe.
Ga bidiyon nan ƙasa:
Banki na zama wani killataccen waje inda mutane ke buɗe asusu domin yin ajiya ta kuɗi. Mutane sun yi amanna da cewa kuɗaɗen su a cikin banki na da cikakken tsaro ta yadda babu mai iya taɓa su.
Sai dai a yanzu zamani ya sauya, domin akwai hanyoyi da yawa da ƴan damfara ke bi suna tafka ta’asa ga asusun ajiyan banki na mutane. Wani lokacin hakan na aukuwa ne tare da haɗin baƙin ma’aikatan bankin, yayin da kuma a wani lokacin sakaci ne da son cin banza ke janyowa mutane na faɗawa tarkon ƴan damfara.
Wannan shine kadan daga rahotan wacca ak wawure mata kudi a banki rahoto daga shafin Dalatopnews.com
Kada kumanta kudanna mana Alamar kararrawar sanarwa domin samun jin kararrawar sanarwar shirye-shiryenmu Masu ƙayatar wa mungode.