Tir Kashi Anyi Biyan Bashi Da Tsaleliyar Budura

An yi biyan bashi da budurwa a Kano
A karamar hukumar Bichi kuwa wata dambarwa ce ta barke, inda ake zargin wani uba yayi biyan bashi da ‘yar sa a kan kudi naira dubu tamanin.
Budurwa mai suna Rahma Abdurrahman ‘yar shekaru 16 a duniya, inda ta bayyana mana cewa Mahaifinta sun rabu da mahaifiyar ta, kuma yanzu tsawon shekara 7 kenan da mahaifin ya rabata da mahaifiyar ta, inda ya kai ta garin Zaria, babu makarantar Allo balantana ta boko. Hassalima babban aikin ta safe zuwa dare shi ne yin noman masara da shinkafa.
Ana wannan zaman ne sai mahaifin ya nemi bayar da ita aure gun wani da yake binsa bashin naira dubu tamanin a don haka zai yi biyan bashi da ita.
A yayin da ake tsaka da shirye-shiryen shagalin wannan aure ne sai Rahma ta gudo zuwa Bichi wurin mahaifiyar ta.
Wane tudu wane gangare shi kuma maihaifin na ta sai yayi tattaki daga Zaria zuwa Bichin, ya kuma shigar da karar mahaifiyar Rahman a wurin jami’an tsaro cewa ta sace masa ‘yar sa inda akai zargin sun yi musu sulhu, suka yi sulhu a tsakanin su, inji mahaifiyar Rahman mai suna Sahura Halilu, amma ta ce daga baya mahaifin Rahman wato tsohon mai gidan nata, ya sake shigar da ita kara a gaban kotun shari’ar musulunci dake garin Bichi, kan wancan zargin dai na cewar ta sace masa yarinya.
Har ila yau, mahaifiyar Rahma ta sheda mana cewa,tun bayan da mahaifin su Rahma ya tattara yaranta ya tafi dasu kuma koda ta je zuwan farko domin duba halin da suke ciki, sai ya fada mata cewa kada ta kuskura ta kara zuwa inda ya ke shi da ‘ya’yan sa.
Kazalika ya yi mata ikrarin cewa akwai wani kulumboto da ya yi wanda har abada ba zata taba yin aure ba.
Yanzu haka dai tuni wata lauya mai fafutukar kare hakkin al’umma, Barista Hadiza Nasir Ahmad ta shiga wannan shari’a domin bayar da kariya ga wannan budurwa da mahaifiyar ta, Barista dai ta ce wannan aure da ake shirin yi ya saba da tsari irin na addinin Islama.
Shi ma a nasa bangaren mahaifin wannan Budurwa Alhaji Abdurrahman ya ce ko kadan ba haka wannan zance yake ba, domin kuwa bashi da labarin auren biyan bashin game da ‘yar tasa, ya dai san cewa a baya ya yi shirin yi mata auren zumunci amma ba auren bashi ba bane.
Dangane da ikrarin mahaifiyar Rahma kuwa na cewa Malam Abdurrahman din ya yi wani kulumboto, ya ce shi fa dogaron sa Allah.