Wani Abin ƙunya Wata Mata Ta Kashe Aurenta Ta Auri Saurayin ‘Yarta A jihar Kano

0

Innalilahi Abin ƙunya Wata Mata Ta Kashe Aurenta Ta Auri Saurayin ‘Yarta A jihar Kano

Wata mata mai suna Khadijah dake zaune a ƙaramar hukumar Rano ta jihar Kano ta kashe aurenta inda ta auri saurayin ‘yarta.

Tun da farko dai, wani mutum ne mai suna Usman ya nemi auren A’isha, wato ‘yar Khadijah, amma magabatanta suka ga ba su amince da nagartarsa ba don haka suka ce sam wannan mutum ba zai auri ‘yarsa ba, kamar yadda rahoton In Da Ranka na Freedom Radio Kano ya bayyana.

Ana haka ne sai Khadijah ta ce ita fa ta amince da nagartar Usman, wato saurayin da yake neman ‘yar tata.

Haka ne ya sa mahaifiyar A’isha ta kashe aurenta don ta auri Usman.

Iyayen Khadijah dai sun nuna ƙin amincewa da wannan aure da take so ta yi, abin da ya sa ta garzaya wajen Kwamandan Hisbah na Rano, inda ya ɗaura mata aure.

Maɗaurin aurenta, Abdullahi Juma Rano, ya ce su fa ba su amince da wannan aure ba.

Related Posts
1 of 405

“Mu ba mu yadda ba, sai ta tafi wajen Kwamandan Hisbah na Rano suka yi ƙara. Kwamandan Hisbah ya kira miji, yana Mina, ta waya, ya ce lallai sai ya sake ta. Ya ce a shi ba zai sake ta ba. Shi ne Kwamandan Hisbah ya ce ya ba shi sati ɗaya.

“Da sati ya cika aka koma, saboda haka ya sake ta. Ita kuma dama sun gama daidaitawa da saurayin ‘yarta akan lallai sai ta kashe aure.

“Bayan ta zo ta kashe aure, ta je suka yi abin da za su yi, ta kawo mana shi gidanmu akan mu ɗaura mata aure da shi. Muka ce mu. Muka ce mu mun san tun da aurenki yake neman ki, don haka mu ba za mu ɗaura miki aure da shi ba”, in ji Ɗan kuma.

Naziru Juma Rano, wanda ɗan uwa ne shaƙiƙi, ya yi kira ga Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje da Kwamandan Hisbah na Jihar Kano, Harun Muhammad Ibn Sina da su shiga maganar domin su a yanzu ma ba su san ina amaryar take ba.

Ita kuwa amarya, ta ce ita fa ta tambayi malamai akan wannan auren nata kuma sun ce ba haram ba ne.

“Ni na tambayi malamanmu tun da sun ce ba haramun ba ne, amam ni ku tambaya mini. Aka tambaya aka ce ba haramun ba ne na zo na sanar da iyayeshi. Iyayenshi suka neme shi suka sanar da shi.

“Suka ce to ba matsala. Duk abin da suka gani shari’a bai saɓa ma abin ba saboda haka duk abin da suka ce shi zai yi.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More

Privacy & Cookies Policy