Wani Bahaushe Mai Suna Abdukadir Tare Da Matar Sa Halimato Sun Haifi ‘Ya’ya 19 A Rana Guda
Masha Allah Wani Bahaushe Mai Suna Abdukadir Tare Da Matar Sa Halimato Sun Haifi ‘Ya’ya 19 A Rana Guda
MAWAKI DAVIDO YAYI ABIN KIRKI.
Satin da ya wuce mawakin zamani Davido ya ajiye account numbe dinsa yace masoyansa su bashi kyautar kudi saboda ranar murnan haihuwarsa
Mawakin yace zuwa yanzu an tura masa kyautar kudi Naira Milyan dari biyu (200,000,000).
Amma abin mamaki mawakin yaceba zaici ko kobo ba a cikin kudin ya sadaukar wa marayu, har ma yace ya kara Naira Miliyan hamsin (50,000,000) sadaukar wa ga marayu daga aljihunsa, kudi ya zama Miliyan dari biyu da hamsin za’a rabawa marayu
Ya kafa kwamitin da zasuyi aikin raba kudin a gidajen marayu dake fadin tarayyar Nigeria, yace da zaran an gama tantance gidajen marayun za’a tura kudin kai tsaye zuwa ga asusun ajiyar kudi na gidan marayun.
Cikin kwamitin da ya kafa babu Musulmi ko guda daya, don haka kar ma kuyi tsammanin zasu saka gidan marayu na Musulmai a cikin kason kudin.
Idan mutum kamar Davido zai iya tara wannan kudin ya rabawa marayu ‘yan uwansa shin me ya hana attajirai ‘yan Arewa Musulmai suyi irin wannan domin su taimaki nasu marayun?
Davido kam yayi abin kirki, abin kwaikwayo ga duk wanda ya samu iko da dama na taimakon marayu.
Allah Ka bamu ikon taimakon marayu.