Wata Budurwa Ta Baiyana Ra’ayinta Gameda Abinda Ya Faru Da Maryam Booth

Yarinya ta yi rashin kunya amma wai ana ba ta hakuri tare da ba ta kariya, wanda hakan ke nuna alamar goyon baya a gareta.
Maryam ta yi zargin cewa namiji (saurayinta) ne ya dauke ta a bidiyo.
Wanda hakan ke nuni da cewa sun jima suna sharholiya tare. Sannan kuma shi ba mijinta ba, ba dan uwanta ba, amma ya aka yi har ta kai ga ya dauke ta bidiyo tsirara. Wanda hakan ya nuna cewa akwai rashin kunya a lamarin.
Ni abin da yake ba ni mamaki shine yadda ake ta kokarin kare ta. Saboda ban ga dalilin da zai sa a kare ta ba, kamata ya yi a yi Allah wadai da lamarin ba wai a dinga goyon bayan ta ba.
Sako Daga:- Farida Bala