ya mutu kwana 2 da musulunta kuma ya
Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un ya mutu kwana 2 da musulunta kuma ya…
AKWAI ABIN BAN TAUSAYI A CIKIN
Wannan labarin wani yaro ne me kimanin shekara 5 Mahaifiyarsa ta Rasu, sai yaga K
kawai ya dai na ganinta sai ya tambayi babanshi yace: Baba ina mama taje?,
se baban yace: maman ka tana lahira, se yaro yace: yaushe zata dawo? se baban uayi shiru baice komai ba.
Wata rana yaron yana wasa da abokanshi
bayan angama wasa se kowa yace bari yaje
gida gurin maman shi se yaron yace shima
so yake idan ya girma ya samu kudi yaje Lahira don baban shi yace maman sa tana Lahira, se daya daga cikin Abokanensa yace: nima zaka je dani? se yaron yace Ehh.
Wata rana yaron yana makarantar islamiyya malamin su yana wa’azi yana cewa ‘duk wanda ya mutu idan yaje lahira bazai dawo ba’ se yaron ya daga hannu yace malam to idan mutun be dawo ba toh me yakeyi acan?.
Sai malamin yace: Lahira gurine inda ake hisabi ga Matattu kuma duk wanda ya mutu baya dawowa, Sai yaron yace: idan mutun ya mutu ina ake kaishi, se malam yace: Makabarta.
Sai yaron yace: Meyene Mutuwa? Se malamin yace: mutuwa tana nufin fitar Ruhi daga jikin dan Adam,
Sai yaro yace: Toh ina Ruhi yake ajikin dan
Adam? se malam yace kai yaro ka cika
tambaya dayawa, Je ka zauna,
Washe gari bayan sallar Asuba sai yaron yazo gurin babanshi yace ina kwana baba ka tashi lafiya? Baban yace lafiya qalau, se yaron yace baba Inada tambaya, se yace to inajin ka ɗana miye Tambayarka? Se yaron yace: baba Wai ina Ruhin mamana yake? Se baban yayi shiru…………. Can se baban yace: Yaro saurara in baka wani labari Mamanka ta Rasu, Rasuwa kuma idan akayita ba’a dawowa duk wanda aka zarewa Ruhi daga jikinsa bazai rayu ba, lokacin mamanka ne Yayi Shi Yasa Ta rasu, nima idan lokacina yayi Zan mutu na Barka!
Sai yaron yace: Toh baba Don ALLAH idan zaka mutu ka gayamun domin nima inaso Na mutu se In rakaka zuwa gurin mamana naji kewarta wllh baba,
Sai baban yayi shiru don yaga Alamar Yaronnan.Yanason Mamansa kuma yaga Alamar lallai yaron Yana bukatar ganin mamanshi, se babanshi yace je kashirya kazo muje zan kaika inda mamanka take yanzu, .
Sai yaro yaje yayi wanka Yaci kwalliya yana murna zeje gurin mamansa, Dasauri yazo gurin babanshi yace Baba Gani nashirya muje, se baban yakama Hannun yaron
suka fita suna ta tafiya har suka bar Gari
suka shiga daji, suka Isa makabarta, se baban ya nufi Qabarin maman wannan Yaron, Sai
baban yace; Yaro mamanka tana cikin wannan Qasar, Wannan qasar itace Qabari, kuma duk wanda ya mutu a ciki ake sakashi, kuma duk wanda ya mutu baya iya motsi baya iya komai, a haka za’a kawoshi
anan gurin kuma a binneshi baya iya yin
komai se ikon ALLAH, Se yaro ya fashe da
kuka ya fadi qasa yace: Mamana yanzu itace a cikin wannan Qasa?
Sai yace Toh baba wane laifi tayi da ALLAH ya kasheta? Se baban yace kowa haka ze mutu idan lokaci yayi,
Suna zaune se ga wasu mutane sunzo da Gawa za’a binneta a cikin Qabari se yaron ya Qura ido yaga duk yanda ake binne mutun, se suka dawo gida, dasuka dawo gida aduk lokacinda yaron yayi Sallah se yace ALLAH Kaji Qan Mamana!,
yaron ya tara kudin wasa, irin takardun da yara ke kira kudi yakai wa malaminsu yace malam nabaka wannan kudi ne don kayiwa mamana Addua!
Malam yayi shiru yana jin tausayin wannan yaron yace kabar kudin ka zanyiwa mamanka Addua kyauta, yaro cikin kuka yace Nagode!
Yaro Dan Qarami Kenan, Wanda bai mallaki hankalinshi ba! Ina ga kai kuma dake da Hankali???.
Ya Allah kajiqan Iyayenmu, Ka Gafarta Musu Zunubansu, Ka Sanya Aljannna itace Makomarsu!
Don Girman Allah ɗan uwa idan kakaranta katura a groups sabida al’umma su amfana da kai
NASIHOHI GUDA HAMSIN (50)
January 261 ka kula da kanka2 yazamana kana jin tsoron Allah
3 ka san cewa duk abinda ya sameka daga
Allah ne4 ka zamu mai cika alkawari5 ka zauna da kowa lafiya
6 ka dinga tunawa da mutuwa
7 ka rage buri
B ka cire kwadayi
9 banda yin hassada don kaga Allah yadaukaka wani10 kasan cewa ita fa duniya ba matabbaciyabace11 ka yawaita istigifari
12 ka yawaita salati ga manzon Rahama
13 banda yin gulma ko munafurci14 banda cin amana15 ka zauna da kowa lafiya
16 ka tsarkaka zuciyarka17 banda nufar mutum da sharri18 karkayi zalunci
19 karkayi girman kai
20 karkayi wulakanci21 ka zama mai taimako22 ka kula da addininka23 ka zamu mutum mai Alkunya
24 ka zama mutum naqari mai kirki
25 kasan cewa komai mai wucewa ne26 ka dinga hakuri kar ama shaidar cewabaka da hakuri27 ka kuma yawaita addu’a
28 kayi biyyah ga iyayenka
29 ka zama mai tausayi30 ka zama mai imani31 kana aiki da hankalinka32 ka guje wa sabon Allah33 karka ci haram34 karkayi shaye-shaye35 ka nisanci zina36 ka mai da hankalinka guri daya
37 ka ciyar da kanka halal 38 karka zama mutum mai yaudara 38 karka zama mutum mai yaudara
39 duk abinda zakayi kayi saboda Allah
40 banda aibatan mutum don kaga yana
wani yanayi.yi mishi addu’a
41 ka zama mai taimako da tausayin
iyayenka
42 ka yawaita yiwa wadanda suka rasuaddu’a43 kazama mutumin da kowa zai dinga
maka kyakkyawar shaida
44 kabi duniya a hankali
45 karka dinga yin gaggawa
46 sannan ka rike gaskiya duk maganar
dazaka fada kake yin gaskiya.47 ka zamu mai adalci a duk inda kake48 kar abin duniya ya rudeka har kaje kanaaikata sabo49 ka kula da hakkin makwaftanka50 kayi fatan gamawa da duniya lafiya…Allaah Yasa mudace..Dan darajar Annabi Muhammad (S.A W)
Kayi share zuwa groups 5 kacal sannan kayi
Adding dina.